Kwanan nan Sojoji za su ga karshen Turji – Gwamnan Sokoto ya yi albishir a 2022

Kwanan nan Sojoji za su ga karshen Turji – Gwamnan Sokoto ya yi albishir a 2022

  • Mai girma Gwamnan jihar Sokoto ya yi alkawarin cewa an kusa kawo karshen ta’adin Bello Turji
  • Rt. Hon. Aminu Tambuwal ya yi zama da manyan yankin gabashin Sokoto bayan harin da aka kai
  • Gwamnan ya kafa kwamitin Sokoto Eastern Zone Development Association da za su bada gudumuwa

Sokoto - Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya sha alwashi cewa karshen gawurtaccen ‘dan bindiga, Bello Turji ya na daf da zuwa karshe.

Premium Times ta rahoto Mai girma gwamnan ya na wannan bayani lokacin da ya zanta da shugabannin al’umma a ranar Asabar, 1 ga watan Junairu, 2022.

Aminu Waziri Tambuwal ya yi zama na musamman da al’ummarsa ne a sakamakon wani hari da aka kai a yankin Sabon Birni, inda aka kashe wani ‘dan kasuwa.

Baya ga kisan ‘dan kasuwan, ‘yan bindiga sun yi awon-gaba da mutane biyar a kayen Kurawa. Gwamnan ya bayyana masu irin kokarin da gwamnati ta ke yi.

Kara karanta wannan

Da zafi-zafi: Ganduje ya yi martani mai zafi ga Kwankwaso kan zargin murde zaben 2019

Gwamna Aminu Tambuwal ya shaidawa shugabannin al’ummar da suka fito daga gabashin jihar ta Sokoto cewa sojojin kasa sun kusa ganin bayan Bello Turji.

Gwamnan Sokoto
Aminu Waziri Tambuwal da Bello Turji Hoto: www.kanyidaily.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bello Turji ya gagara

Ana zargin cewa Bello Turji da yaransa ne suka addabi mafi yawan kauyukan da suke yankin Isa, Sabon Birni, Gwaranyo, Raba, da kuma Wurno a jihar Sokoto.

Jaridar ta rahoto cewa gwamnan ya rantsar da kungiyar Sokoto Eastern Zone Development Association da za ta taimakawa gwamnati a magance matsalar tsaro.

Rt. Hon. Aminu Tambuwal yace dole a hada-kai

“Wannan ba taron siyasa ko addini ba ne. Mun zauna domin mu fadawa kanmu gaskiya ne.”
Ba za mu zura ido mu na jira gwamnati ta yi mana maganin dukkanin matsalolinmu ba. Dole mu hada-kai, mu taimaki juna, kafin gwamnati ta shigo ciki”

Kara karanta wannan

Daga karshe: Shehu Sani ya bayyana aniyar tsayawa takarar gwamna, ya fadi manufarsa

“Gwamnati ta taimakawa jami’an tsaro da motoci da babura, kuma mu na yin zama da su.”
“Daga cikin aikin wannan kwamiti shi ne ta tabbatar da an kula da dukiyar gwamnati, an sa ido kuma an tabbatar da cewa an yi amfani da su inda suka dace.”

- Aminu Tambuwal

Nasarori 100 da muka samu a 2021 - Buhari

A karshen shekarar 2021 ne Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta jero irin nasarorin da ta samu a shekarar nan ta 2021, daga ciki har da bangaren tsaro.

Jerin da Lai Mohammed ya kawo ya fara ne da irin nasarorin da jami’an tsaro suka samu a kan ‘yan bindiga da sauran ‘yan ta’ddan da suke tada kayar-baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel