Yanzu nan: Shugaban kasa Buhari da Jonathan sun sa labule a fadar Aso Rock Villa

Yanzu nan: Shugaban kasa Buhari da Jonathan sun sa labule a fadar Aso Rock Villa

  • Tsohon shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan ya ziyarci fadar Aso Rock Villa da yammacin yau
  • Watakila haduwar ta su a yau ranar 30 ga watan Disamba, 2021 ita ce zaman su ta karshe a 2021
  • Hadimin shugaban Najeriya ya tabbatar da haduwar, amma ba a san dalilin tattaunawar ta su ba

Mai girma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya na ganawa da tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan.

Rahotanni daga majiyoyi dabam-dabam sun tabbatar da cewa Dr. Goodluck Jonathan ya ziyarci fadar shugaban kasa.

Vanguard tace Jonathan ya ziyarci Aso Rock Villa ne da kimanin karfe 3:00 na yau Alhamis, 30 ga watan Disamba.

Har zuwa yanzu ba a samu labarin abin da tsohon shugaban na Najeriya da magajin na sa suka tattauna a kai ba.

Sai dai Dr. Jonathan ya saba ganawa da shugaban kasa inda yake sanar da shi game da aikin da yake yi wa ECOWAS.

Fadar Aso Rock Villa
Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan Hoto: @bashahmad
Asali: Facebook

Tsohon shugaban kasar ne aka zaba domin ya zama jakada na musamman domin sasanta rikicin siyasar kasar Mali.

Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmaad ya tabbatar da wannan ganawa a shafinsa na Facebook dazu da rana.

Mai taimakawa Muhammadu Buhari wajen kafofin sadarwa na zamani yace mai gidan na sa ya gana da Jonathan.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Goodluck Jonathan yau a fadar shugaban kasa, Abuja.

Kamar yada Punch ta kawo rahoto, an yi tattaunawar ne ta bayan labule ba tare da an samu sakamakon ganawar.

Kungiyar Arewa ta na kuka

Gamayyar Kungiyoyin Arewa ta CNG ta koka kan matsalar kashe-kashe, da garkuwa da mutane, da rashin tsaro.

CNG tace ya kamata shugaba Buhari ya dawo da Najeriya yadda ya same ta a hannun Goodluck Jonathan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel