Yadda ɗan gani kashenin Buhari ya koma Kwankwasiyya bayan ƴan bindiga sun sace ƴan uwansa 5

Yadda ɗan gani kashenin Buhari ya koma Kwankwasiyya bayan ƴan bindiga sun sace ƴan uwansa 5

  • Sirajo Saidu, wani dan kanzagin Buhari wanda ya ke nuna goyon bayansa a shafinsa na Facebook ya bayyana batun sauya shekarsu zuwa mabiyin Rabiu Kwankwaso
  • Hakan ya biyo bayan yadda ya dade yana nuna goyon baya ga Buhari na tsawon lokaci amma daga bisani masu garkuwa da mutane su ka sace ‘yan uwansa na jini guda biyar
  • An samu bayanai akan yadda masu garkuwa da mutane su ka je har karamar hukumar Wurno da ke jihar Sokoto, garinsu Saidu a ranar 12 ga watan Disamba inda su ka sace mutane 20

Sokoto - Wani dan gani kashenin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana sauya shekarsa a shafinsa na Facebook.

Ya bayyana cewa yanzu ya koma bayan tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Babban hadimin tsohon Gwamna Okorocha ya karyata zargin wata alaka da ‘Yan bindiga

Yadda ɗan gani kashenin Buhari ya koma Kwankwasiyya bayan ƴan bindiga sun sace ƴan uwansa 5
Dan gani kashe nin Buhari ya koma Kwankwasiyya. Hoto: Sirajo Sa Idu Sokoto
Asali: Facebook

Saidu wanda dan asalin jihar Sokoto ne, ya bayyana yadda ya sauya sheka bayan masu garkuwa da mutane sun sace ‘yan uwansa 5 na jini.

Premium Times ta bayyana yadda a ranar 12 ga watan Disamba ‘yan bindiga su ka sace mutane 20 sakamakon hare-haren da su ka kai karamar hukumar Wurno da ke jihar Sokoto.

Ya sanar da satan ne ta shafinsa na Facebook

Bayan satan, Saidu ya garzaya shafinsa na Facebook inda ya sanar da satan ‘yar uwansa maza 5 cikin mazaunan da aka sace a yankinsu.

“Duk maza guda 5 da aka sace a gidanmu ‘yan uwana ne. ‘Yan bindiga ba su halaka kowa ba amma sun sace ‘jama’a. Mu na jiransu (‘yan bindigan) su kira mu don amsar kudin fansa. Ku taimaka ku saka ‘yan uwana da sauran wadanda aka sace a addu’a”, kamar yadda ya wallafa.

Kara karanta wannan

Jami’an tsaro sun gaza, Gwamnan Arewa ya sake ba Talakawa shawara su tanadi bindigogi

Yayin tattaunawa da Premium Times bayan kwana biyu da satar, Saidu ya ce masu garkuwa da mutanen sun kira ‘yan uwa inda su ka bukaci kudin fansa wanda yanzu haka an fara tattarawa. Amma bai sanar da yawan kudin ba.

Na koma bayan Kwankwaso

Yayin da jama’a su ka koma sukarsa a Facebook, ya ce ya koma PDP domin babu wani dan APC da ya tallafa masa wurin ceto ‘yan uwansa ko da da sisin kwabo ne.

Yadda ɗan gani kashenin Buhari ya koma Kwankwasiyya bayan ƴan bindiga sun sace ƴan uwansa 5
Bayan sace 'yan uwansa 5, mai goyon bayan Buhari ya koma Kwankwasiyya. Hoto: Sirajo Sa Idu Sokoto
Asali: Facebook

Kamar yadda ya wallafa:

“Daga yau ranar Laraba, 29 ga watan Disamban 2021, Ni Surajo Saidu Sokoto na bar Buhariyya yanzu na koma Kwankwasiyyya. Saboda bayan na bayyana satar ‘yan uwana a Facebook babu wanda ya tallafa min da kudi ko kuma ya ceto su.”

Nan da nan ya maye gurbin hoton Buhari da ke shafinsa na Facebook da na Kwankwaso.

Kwankwaso tsohon gwamnan jihar Kano ne kuma dan PDP ne. Ya nemi takarar shugabancin kasa amma Atiku ya kayar da shi tun a zaben fitar da gwani na jam’iyya.

Kara karanta wannan

Akwai hannun Gwamnoni wajen kawowa Buhari matsalar tsaro inji Tsohon Shugaban Majalisa

Dama ya dade yana wallafe-wallafe iri-iri masu kawo cece-kuce

A baya Sirajo ya taba wallafa cewa ‘yan jaridan Najeriya mikiyan Buhari ne kuma su ne masu kawo cikas a mulkin Buhari.

Ya taba cewa zai raka jami’an SSS gida-gida don kama makiyan Buhari da ke cikin jihar Sokoto.

Bayan wannan wallafar akwai wasu da dama da yayi wanda za ka ga mutane da dama su na caccakarsa saboda yadda yake nuna goyon baya ga Buhari duk da halin tsananin da kasa take ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel