Da Dumi-Dumi: Gwamnati Tarayyar Najeriya ta bayar da garabasar hawa jiragen kasa kyauta na mako guda

Da Dumi-Dumi: Gwamnati Tarayyar Najeriya ta bayar da garabasar hawa jiragen kasa kyauta na mako guda

  • Gwamnatin tarayya ta ce kowa ya hau jirgin kasa a kyauta tun daga ranar Juma’a, 24 ga watan Disamba zuwa 4 ga watan Janairun 2022
  • Kakakin kamfanonin sufurin jiragen kasan Najeriya, NRC Mahmood Yakubu ya bayyana hakan ta wata takarda ya saki
  • A cewarsa, gwamnatin ta bayar da wannan garabasar ne don tallafa wa matafiya cikin lokacin bukukuwan karshen shekarar nan

Gwamnatin tarayya ta bayar da garabasar hawa jiragen kasa a Najeriya tun daga ranar Juma’a 24 ga watan Disamba har zuwa ranar 4 ga watan Janairun 2022, Daily Trust ta ruwaito.

Kakakin kamfanonin sufurin jiragen kasa na Najeriya (NRC), Mr Mahmood Yakub ya bayyana hakan ta wata takarda.

Da Dumi-Dumi: Gwamnati Tarayyar Najeriya ta bayar da garabasar hawa jiragen kasa kyauta na mako guda
FG ta bawa 'yan Najeriya garabasar hawa jirgin kasa kyauta na mako guda. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Yadda Gwamnoni 6 suka hana Majalisa juyawa Shugaban kasa baya a kan kudirin gyara zabe

A cewarsa kyauta ko wacce tashar jirgi za ta dauki mutane da kayansu a duk fadin kasar nan.

Daily Trust ta bayyana tashoshin inda ta ce sun kunshi tashar jirgin kasa ta Abuja zuwa Kaduna, Legas zuwa Ibadan, Warri zuwa Itakpe, Kano zuwa Legas, Minna zuwa Kaduna da Aba zuwa Port Harcourt.

Ya ce hakan zai taimaka wa jama’a da dama wurin zuwa wuraren da suke so

Darektan NRC, Injiniya Fidet Okhira, wanda ya bayar da wannan sanarwar ya ce:

“An dauki wannan matakin ne bisa hadin kan ma’aikatar sufuri ta kasa don tallafa wa jama’an Najeriya a lokacin bukukuwan karshen shakerar nan.
“Hakan zai taimaka wurin rage wa jama’a kudin sufuri yadda kowa zai je inda ya ke son zuwa cikin lokacin nan."

Ya ce fasinjoji su kiyaye dokokin COVID-19

Ya kara da shawartar fasinjoji da su tanadi tikitinsu a wuraren da ya kamata ba tare da biya ko sisi ba don samun damar shiga jiragen.

Kara karanta wannan

Matasan Arewa sun tura sako ga gwamnatin Buhari kan lamarin 'yan bindiga

Ya kara da cewa ko wanne fasinja ya kula kuma ya kiyaye dokar COVID-19 ta hanyar sa takunkumin fuska, wanke hannaye da amfani da sinadarin kashe kwayoyin cutuka.

Ya kuma sanar da kokarin gwamnatin tarayya wurin tabbatar da lafiya da dukiyoyin fasinjoji ta hanyar samar da tsaro a filayen jiragen cikin wannan lokaci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel