Bayan Legas, an samu Gwamnan Arewa da zai gwangwaje ma’aikata da kudin karshen shekara

Bayan Legas, an samu Gwamnan Arewa da zai gwangwaje ma’aikata da kudin karshen shekara

  • Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai yace za a biya ma’aikata kyautan kudin karshen shekara
  • Malam Nasir El-Rufai yace kowane ma’aikaci da ke jihar Kaduna zai amfana da wannan kyauta
  • Muyiwa Adekeye yace Gwamnatin Kaduna za ta kashe sama da Naira biliyan 1.3 a kan wannan

Kaduna – Mai girma Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya amince a biya ma’aikata kyautar kudi a matsayin tukwuicin karshen shekara.

Malam Nasir El-Rufai ya bada wannan sanarwa ne a wani sako da ya fitar ta bakin hadiminsa, Muyiwa Adekeye a ranar 21 ga watan Disamba, 2021.

A wannan sanarwa mai taken “KDSG approves bonus for civil servants”, gwamnan yace ma’aikata za su samu kyautar kudi daidai da matsayinsu.

“Ma’aikatan gwamnati za su tashi da kyautar kudi daga 100% ga kananan ma’aikata zuwa 30% ga kananan ma’aikata.” - Muyiwa Adekeye.

Kara karanta wannan

El-Rufai ya tura sako ga 'yan Kaduna, ya ce su gaggauta cika shirin tallafin Korona

Meyasa za a rabawa ma'aikata 'bonus'?

Sanarwar da ta fito daga gidan gwamnati na Sir Kashim Ibrahim House ya bayyana cewa za a raba wadannan kudi ne domin a zaburar da ma’aikata.

Gwamnan jihar Kaduna
Gwamnan jihar Kaduna da mukarrabansa Hoto: @GovKaduna
Asali: Facebook

A karkashin wannan tsari, ma’aikatan da suke kan mataki na 1 zuwa na 7, za su samu kyautar 100% na albashin da suka saba karba a kowane wata.

Kamar yadda Adekeye ya yi bayani, ma’aikatan da suke tsaka-tsakiya a ofis, watau wadanda suke matsayi na 8 zuwa 13 za su samu 40% na albashinsu.

Manyan ma’aikata da suke mataki na 14 za su karbi 40% na abin da suke karba a kowane wata.

Kokarin gwamnatin El-Rufai

Wannan kyauta da gwamnatin jihar Kaduna za tayi wa ma’aikatan zai ci Naira biliyan 1.382. Hakan na zuwa ne bayan irin kokarin da El-Rufai yake yi.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya rabawa 'yan mazabarsa motoci 50, babura 500 da kayan gona a tashi daya

Mai taimakawa gwamnan wajen yada labarai yace a 2019, Kaduna ta zama jihar farko da ta fara biyan ma’aikata sabon tsarin albashin N30, 000 a Najeriya.

Ma'aikatan Legas za su samu kyautan kudi

A makon da ya gabata an ji cewa Gwamnatin Babajide Sanwo-Olu a jihar Legas za ta biya duk wani ma’aikacin jihar alawus na karshen shekarar nan ta 2021.

Ma’aikatan kananan hukumomi da malaman makaranta za su samu 30% na albashinsu a Disamba

Asali: Legit.ng

Online view pixel