Mai binciken kudi ya fallasa yadda ma’aikatan bogi suka sulale da miliyoyi a asibitin FMC

Mai binciken kudi ya fallasa yadda ma’aikatan bogi suka sulale da miliyoyi a asibitin FMC

  • Ofishin mai binciken kudin gwamnatin tarayya ya fallasa badakalar da aka yi a asibitin FMC Keffi
  • Rahoton binciken 2019 ya nuna cewa an yi gaba da Naira biliyan 229 wajen biyan ma’aikatan bogi
  • Shugabannin asibitin sun ce an samu matsala ne ta sanadiyyar amfani da manhajar albashin GIFMIS

Abuja - Mai binciken kudin gwamnatin tarayya ya zargi shugabannin asibitin FMC na garin Keffi, jihar Nasarawa da biyan N229m ga ma’aikatan bogi.

Premium Times tace rahoton binciken ya nuna an batar da wadannan kudi ne tsakanin 2016 da 2019.

Wannan ya na cikin binciken da ofishin mai binciken kudin gwamnatin tarayya ta yi a shekarar 2019, aka samu wasu ma’aikatun tarayya da saba doka.

Rahoton na 2019 ya nuna N229, 391,842 sun tafi da sunan biyan ma’aikatan bogi albashi. An fitar da wannan kudi ta manhajar GIFMIS a shekarar 2016.

Kara karanta wannan

An titsiye ministocin Najeriya, sun kasa bayani kan inda N324bn ya tafi - Rahoto

Daga cikin wadannan ma’aikata na bogi, akwai wanda aka biya albashi sau tara a rana daya.

Minister of health
Ministan lafiya na kasa, @fmohnigeria
Asali: Twitter

Da jaridar Premium Times tayi bincike, ta gano cewa duk a cikin sunayen wadanda aka rika turawa wadannan miliyoyin kudi, babu wani ma’aikacin kwarai.

Har ila yau, rahoton ya fallasa yadda asibitin ya karkatar da Naira biliyan 4.2 daga cikin kudin ma’aikata. An karkatar da kudin a shekarar 2016, 2017 da 2018.

An gano an kashe sama da Naira biliyan 1.3 ta irin wannan yanayi a wannan shekaru Bayan haka akwai wasu Naira biliyan 2.8 da suka shiga aljihun wasu jami'ai.

Martanin gwamnatin tarayya

Wannan danyen aiki da aka yi ya saba doka, kuma mai binciken kudin gwamnatin tarayya ya bada shawarar hukumar EFCC ta binciki wanda aka samu da laifi.

Kara karanta wannan

An karrama dan Najeriyan da mayar da kudi N11m da ya tsinta a Dubai

Shugabannin asibitin sun daura laifin a kan GIFMIS, suka ce babu wani ma’aikacin bogi da ke asibitin.

Gwamnatin Muhammadu Buhari ta shigo da tsarin IPPIS da nufin a kauda ma’aikatan bogi. Hakan ya taimakawa gwamnatin tarayya ta adana dala miliyan 500.

Badakala a ma'aikatar shari'a

An gano an karkatar da kudin yin ayyuka na sama da N35m, kuma an biya ‘yan kwangila N53m ba tare da bin doka ba a ma'aikatar tarayya ta shari'a a Najeriya.

Rahoton binciken da aka yi ya nuna an kashe makudan kudi ba tare da an tanadi takardu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel