Bincike ya tona yadda aka yi ta wawurar miliyoyin kudi a ma’aikatar tarayya a shekarar 2019

Bincike ya tona yadda aka yi ta wawurar miliyoyin kudi a ma’aikatar tarayya a shekarar 2019

  • Rahoton binciken OAuGF ya zargi ma’aikatar shari’a da karkatar da har sama da Naira miliyan 113
  • Binciken kudin da aka yi ya nuna yadda aka rika sabawa ka’idoji da sharudan aiki a ma’aikatar
  • Ma’aikatar shari’a ta amsa laifinta, inda ta rika cewa kuskure aka samu, ko ba ta san da dokokin ba

Abuja – Bincike ya nuna cewa a shekarar 2019, ma’aikatar shari’a ta tarayya ta kashe sama da Naira miliyan 113 ba tare da bin dokar batar da kudi ba.

Premium Times tace wani rahoto da ofishin mai binciken kudi na kasa watau OAuGF ya fitar, ya nuna yadda ma’aikatar shari’a tayi wa doka karon tsaye.

Rahoton ya zargi ma’aikatar da karkatar da kudin da aka ware da nufin yin ayyuka da kuma biyan ‘yan kwangila kudi ba tare da an tanadi takardu ba.

Kara karanta wannan

An titsiye ministocin Najeriya, sun kasa bayani kan inda N324bn ya tafi - Rahoto

A rahoton da aka fitar, babban mai binciken kudin gwamnatin na kasa yace an wawuri kudin al’umma, an rika kashe su ta hanyar da ba ta dace ba.

An karkatar da kudin yin ayyuka

Sau 12 ana daukar kudi daga kason ayyuka, ana biyan ma’aikata da su a shekarar 2019. Binciken ya nuna adadin kudin da aka karkatar ya haura N35m.

An ware kudin da sunan za a yi ayyuka a ma’aikatar, amma a karshe suka tafi wajen gudanar da taro, horas da ma’aikata, da shirya taron karawa juna sani.

Ministan tarayya
Ministan shari'a, Abubakar Malami SAN Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

An fitar da wasu N53.8m

Har ila yau, binciken da aka yi ya nuna yadda aka biya ‘yan kwangila Naira miliyan 53.8 ba tare da an bi doka ba. Hakan ya na nufin an karkatar da dukiyar kasa.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Buhari ya aminta a biya likitoci albashinsu da aka rike lokacin yajin aiki

Takardun kashe N23.6m sun yi dabo

Jaridar FIJ tace baya ga haka, an kuma nemi takardun da ke nuna yadda aka batar da wasu N23, 581, 944.20 a ma’aikatar shari’ar a shekarar ta 2019, amma an rasa.

Wannan ya sake tozarta yadda ma’aikatar ta ke aiki ba tare da bin ka’idoji da dokokin gwamnati ba.

Amsar da ma’aikatar ta bada

Da take maida martani, ma’aikatar ta wanke kanta daga zargi, tace ta yi gaggawan kashe N53.8m domin maganin wadanda suka shirya zanga-zanga a lokacin.

A kan batun takardun kashe N23.6m da suka bace, ma’aikatar tace kuskure aka samu, sannan tace ba ta san sai kwamiti ya amince kafin a bada kwangila ba.

Aghughu Adolphus ya na ta fasa kwai

A baya kun ji cewa rahoton binciken Aghughu Adolphus ya nuna yadda aka kashe N8.5bn a majalisar dattawa da majalisar wakilai ba tare da bin ka’ida ba.

Akwai kudin da Majalisa ta cire, amma ba su koma cikin asusun gwamnatin tarayya ba har yau

Kara karanta wannan

Sabuwar dokar tattali za ta sa rashin biyan haraji ya kai mutum kurkuku na tsawon shekara 5

Asali: Legit.ng

Online view pixel