Za mu rubuta littafin lakanin kawo karshen matsalolin da ake fama da su - Gwamnoni

Za mu rubuta littafin lakanin kawo karshen matsalolin da ake fama da su - Gwamnoni

Kungiyar Gwamnoni ta cin matsaya cewa za ta rubuta wani littafi a kan maganin matsalolin Najeriya

Gwamnonin jihohin kasar sun bayyana haka a karshen taron da suka yin a ranar 15 ga Disamba, 2021

Wannan littafi zai amfani wadanda za su zama gwamnoni nan gaba da kuma malaman makaranta

Kungiyar NGF ta gwamnonin jihohin Najeriya tace ta tsaida shawarar cewa za su rubuta littafi mai tattare da yadda za a gudanar da mulki a kasar nan.

Jaridar The Cable ta fitar da rahoto a ranar Alhamis, 16 ga watan Disamba, 2021, cewa wannan littafi zai kunshi mafitar matsalolin da ake fama da su.

Gwamnonin sun bayyana haka bayan taron da aka yi ranar Laraba. An gudanar da wannan taro ne ta kafofin yanar gizo ba tare da an shiga dakin taro ba.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 36 sun goyi bayan Buhari a kan janye tallafin mai, a maida litar fetur N340

Kungiyar ta NGF ta ce kowane gwamna zai rubuta irin abubuwan da ya fuskanta a kan mulki matsayin sashen wannan littafi da za su taru, su rubuta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar NGF, wannan littafi zai taimakawa gwamnonin da za su zo nan gaba wajen shawo kan matsalolin da za su iya fuskanta yayin da su ka shiga ofis.

Gwamnoni
Gwamnoni a Kebbi Hoto: www.kebbistate.gov.ng
Asali: UGC

Matsayar NGF bayan taro

“’Ya ‘yan kungiyar sun ci ma matsaya cewa duk za su rubuta sashe guda na littafin da sakatariyar NGF za ta tattara, da hadin-gwiwar Dr. Joe Abah.”
“Littafin zai yi bayanin abubuwan da gwamnoni suka fuskanta. Za a kawo shawawari, mafita da kuma yadda za a bullowa matsalolin shugabanci a Najeriya."
“Littafin zai taimakawa gwamnoni masu zuwa nan gaba, malamai, da daukacin al’umma.” – NGF.

NGF ta saurari shawawarin jama'a

A wannan zama da aka shirya, shugaban gidauniyar Nicky Okoye, da Dr. Nicky Okoye a wasu jami’an gwamnati sun gabatar masu da wasu shawarwari.

Kara karanta wannan

Mawaki ya gwangwaje shugaban 'yan bindiga, Turji, da wakar yabo

Rahoton yace wakilan ma’aikatar kasuwanci da hannun jari sun kawo shawarar yadda za a bi domin a bunkasa sha’anin kananan kasuwanci a kasar nan.

A janye tallafin fetur - NGF

Jihohi za su biya tsofaffin ma’aikata duk wasu fansho da suke bin bashi. Amma gwamnonin za su yi wannan ne idan aka janye tallafin man fetur a shekarar 2022.

Kungiyar Gwamnoni ta bayyana wannan matsaya ne shi ma bayan taro da tayi a makon nan. Kayode Fayemi yace yin hakan zai rage radadin da talaka zai ji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel