Buhari @ 79: Abin da jama'a za su gani kafin Gwamnatin Buhari ta sauka - Gbajabiamilla

Buhari @ 79: Abin da jama'a za su gani kafin Gwamnatin Buhari ta sauka - Gbajabiamilla

A jiya ne Shugaban majalisar wakilan tarayya ya taya Muhammadu Buhari murnar cika shekara 79

Rt. Hon. Femi Gbajabiamila yana ganin ba a taba yin shugaba a Najeriya irin Mai girma Buhari ba

Femi Gbajabiamila yace kafin gwamnati mai-ci ta shude, mutanen kasar nan za su ga ayyuka iri-iri

Abuja - Shugaban majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila, ya taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar cika shekara 79 a ban kasa.

Gidan talabijin na Channels’ TV ya rahoto Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya na cewa ba a taba samun wani shugaba a Najeriya da ya yi ayyuka kamar Buhari ba.

Gbajabiamila yake cewa ya kamata kowane ‘dan kasa mai-kishi ya yi murna da samun irin Buhari saboda irin darajar da martabar da Allah ya yi masa.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban kasa ta jero tulin nasarorin Shugaba Buhari yayin da ya cika shekara 79

Shugaban majalisar wakilan ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya fitar ta bakin hadiminsa, Lanre Lasisi a ranar Alhamis, 16 ga watan Disamba, 2021.

Jawabin yake cewa a shekarunsa a Duniya, Buhari ya yi abubuwa da-dama a matsayinsa na mutum mai zaman kansa da ma shugaba mai daraja da kima.

Buhari da Gbajabiamilla
Buhari, Gbajabiamila a Aso Villa Hoto: thisnigeria.com
Asali: UGC

Gbajabiamila yace ya yi imani cewa shugaban kasar zai yi wa Najeriya ayyuka a shekarun da suka rage masa. Buhari zai bar kan karagar mulki ne a 2023.

This Day tace shugaban majalisar yace ya ji dadin ganin yadda shugaba Buhari yake aiki da takardar alkawuran da jam’iyyar APC tayi wa al’umma a zabe.

Lanre Lasisi ya fitar da jawabi

“Mai girma shugaban kasa, Najeriya da ‘yan Najeriya na alfahari da kai. Yadda kake rike kasar nan, abin a yaba ne.”

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya Na Alfahari Da Buhari, In Ji Kakakin Majalisar Wakilai, Gbajabiamila

“Don haka na shiga cikin sauran masu kishin-kasa, ina taya ka murnar zagayowar ranar haihuwar ta ka.”
“Ina yi maka fatan kara shekaru a Duniya cikin koshin lafiya.” - Femi Gbajabiamilla.

Buhari @79

Shugaban Najeriya ya cika shekaru 79 a Duniya yayin da yake halartar taro a waje. Idan za ku tuna, yanzu haka Muhammadu Buhari ya na wajen taro a Turkiyya.

A lokacin da Buhari zai sauka daga kan mulki a watan Mayun 2023, shekarusa sun kai 80. Hakan ya na nufin shi ne shugaba mafi tsufa da aka yi a tarihin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel