Kan Pantami da Sanatoci ya rabu, Minista ba ya goyon bayan kudirin da Sanatan APC ya kawo

Kan Pantami da Sanatoci ya rabu, Minista ba ya goyon bayan kudirin da Sanatan APC ya kawo

Sanata Adelere Oriolowo ya kawo kudirin da za ta bada dama a kafa makarantar koyar da ICT a Osun

Ministan sadarwa, Isa Ali Ibrahim Pantami ba ya goyon bayan wannan kudiri da aka kai Majalisar

Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami yace gwamnati ba ta da kudin bude wata sabuwar makaranta a yanzu

Abuja - Majalisar dattawa da Ministan sadarwa, Isa Ali Ibrahim Pantami sun samu sabani a kan batun kafa makarantar koyon ilmin ICT a Iwo, jihar Osun.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa matsalar ta faru ne tsakanin Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami da shugaban kwamitin ICT na majalisa, Sanata Yakubu Oseni.

Hakan ya faru ne a lokacin da ake sauraron ra’ayin jama’a a kan kudirin da aka kawo wanda za ta bada dama a kafa makarantar koyar da ilmin ICT a garin Iwo.

Kara karanta wannan

Yanzu kam lokaci ya yi da ya kamata kowa ya nemi makami, gwamna Masari ya magantu

A zaman da aka yi na ranar Alhamis, 16 ga watan Disamba, 2021, kwamitin ya amince a kafa wannan makaranta yadda Sanata Adelere Oriolowo ya nema.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da kamar wahala - Pantami

Amma sai Ministan ya nuna hakan ba za ta yiwu ba saboda matsalar karancin kuri da ake fama da shi, ya kuma ce kafa makarantar za ta zama an yi mai-mai.

Sanatoci
Wani kwamitin majalisa ya na zama Hoto: @TheSenatePresident/TopeBrown
Asali: Facebook

A rahoton da Punch ta fitar, Isa Ali Ibrahim Pantami yana ganin akwai wasu makarantun birjik a Najeriya da suke yi irin abin da wannan makarantar da za tayi.

Makarantar ta na da amfani - Adelere Oriolowo

Shi dai Sanatan na Osun ya yamma, Adelere Oriolowo yace kafa wannan makaranta za ta taimaka wajen yin bincike da koyar da ilmin ICT a zamanin nan na yau.

Sanata Oriolowo ya ce kasashen Duniya sun cigaba a fannin ICT, don haka yake ganin samun irin makaranta za ta taimaka a harkar aikin jarida da samar da tsaro.

Kara karanta wannan

'Yan Majalisan Arewa sun sa dole Sanatar Ekiti ta janye kudirin da zai daidaita mata da maza

Bitrus Bako ya wakilci Dr. Isa Pantami a Majalisa

Sakataren din-din-din na ma’aikatar sadarwa, Bitrus Bako ya wakilci Mai girma Ministan a wajen zaman, yace a halin yanzu ba a bukatar wannan makaranta.

“Duk da yadda kafa makarantar take da amfani, idan har an kafa ta, za ta gamu da matsalar karancin kudi kamar yadda sauran makarantu suke fama.”
“Wani abin lura kuma shi ne, akwai makarantun koyon aiki da suke karantar da irin darusan da ake so wannan cibiya ta rika koyarwa idan an kafa ta.”
“Maimakon ayi ta kafa sababbin makarantu, a maida hankali wajen kula da wadanda ake da su. Ma’aikata ta na bada shawarar a janye kudirin.” – Bako.

'Dan Majalisa ya mutu a Kaduna

Idan za a tuna, 'yan bindiga sun hallaka daya daga cikin ‘yan majalisar dokokin jihar Kaduna. Rilwanu Gadagau shi ne 'dan majalisa mai wakiltar Giwa ta yamma.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari hazikar dalibata ce a darasin Physics, Malamar uwargidan shugaban kasa

Gadagau shi ne ‘Dan Majalisa na biyu da ya fada tarkon ‘Yan bindiga a hanyar Zaria. Kafin nan akwai lokacin da aka sace ‘dan majalisar Zaria, Hon. Sulaiman Dabo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel