Masari da Ganduje: Lokaci ya yi da za mu daina wannan wasan, mu yaki 'yan bindiga

Masari da Ganduje: Lokaci ya yi da za mu daina wannan wasan, mu yaki 'yan bindiga

  • Kungiyar gwamnonin arewa maso gabas sun dira birnin tarayya domin ta'aziyya ga gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar
  • Gwamnonin sun bayyana cewa lokaci ya yi da za su daina dora wa juna laifi sannan su tashi tare da yaki da ta'addancin da ya addabi yakin
  • Kamar yadda shugaban kungiyar, Gwamna Aminu Bello Masari ya sanar, ya ce dole ne masu ruwa da tsaki su tashi saboda magance matsalar 'yan bindiga

Abuja - Kungiyar gwamnonin arewa maso yamma ta ce domin samun ganin bayan ta'addancin 'yan bindiga, dole ne masu ruwa da tsaki su mayar da hankali wurin yakar matsalar.

Daily Trust ta ruwaito, Shugaban kungiyar, Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya sanar da hakan a ranar Alhamis a Abuja yayin da ya jagoranci wakilan kungiyar domin gaisuwar ta'aziyya ga Sanata Aliyu Wamakko.

Kara karanta wannan

Yanzu kam lokaci ya yi da ya kamata kowa ya nemi makami, gwamna Masari ya magantu

Masari da Ganduje: Lokaci ya yi da za mu daina wannan wasan, mu yaki 'yan bindiga
Masari da Ganduje: Lokaci ya yi da za mu daina wannan wasan, mu yaki 'yan bindiga. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: UGC

'Yan bindiga sun kashe wasu daga cikin 'yan jihar Sokoto tare da rufe wasu da banka musu wuta a mota.

Ya ce: "Mun zo jihar Sokoto domin jajantawa ga gwamnati da kuma iyalan wadanda aka kashe da sunan ta'addanci a jihar.
"Matsalar 'yan bindiga a yankin arewa maso yamma na kasar nan ya fi karfin mu. Mun san cewa matsalar da a shawo kan duk abu ne da za mu iya. A don haka ne dole dukkanmu ma tashi tsaya tare da daina dora wa juna laifi."
“Ta'addancin 'yan bindiga, ballantana a yankinmu na arewa maso yammacin kasar nan zai iya magantuwa a cikin sauki idan har dukkanmu mun hada kai.
"Wannan al'amarin bashi da alaka da addini, kabila ko kuma akida. Wannan kawai ta'addanci ne tsagwaronsa," yace.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: Miyagun Yan bindiga sun kuma sace wani Sarki a Najeriya

Jami'an 'yan sanda suna da iyakoki

A yayin tabbatar da cewa 'yan sandan Najeriya suna da iyakoki wurin yaki da rashin tsaro, Masari ya ce cibiyoyin tsaro suna bukatar fasahohi na yaki da kalubale, Punch ta ruwaito.

"Ya dace mu san daga inda ake saukan 'yan bindigan aiki, da mene ake biyansu, dukkan wadannan abubuwan ya dace mu sani su.
"Wadannan sune abubuwan da ya dace muna da karfin aikatawa, akwai shugabancin da kuma siyasa." yace.

Sarkin Musulmi ya ja kunne kan siyasantar da rashin tsaro, ya ce yunwa ba ta san addini ba

A wani labari na daban, sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar, ya ja kunne akan kada shugabannin addinai da 'yan siyasa su mayar da matsalar tsaron Najeriya ta siyasa.

Ana ta samun karin rashin tsaro, ta’addanci da sauran ayyukan assha yayin da ‘yan bindiga da sauran ‘yan ta’adda su ke cin karensu babu babbaka a arewa maso yamma, arewa maso gabas da sauran bangarori.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya ja kunne kan siyasantar da rashin tsaro, ya ce yunwa ba ta san addini ba

Akwai mutane da dama da aka halaka, aka yi garkuwa da su sannan wasu aka yi musu fyade, Channels TV ta ruwaito hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel