Gwamna ya shiga shaukin soyayya, ya zuba kalamai masu ratsa zuciya domin taya matarsa murna

Gwamna ya shiga shaukin soyayya, ya zuba kalamai masu ratsa zuciya domin taya matarsa murna

  • Matukar an gina soyayya ta gaskiya kafin aure, to ko mi daren daɗewa wannan soyayyar zata cigaba da karuwa ne ko bayan an zama ɗaya
  • Gwamnan Imo, Hope Uzodimma, ya zama misali, inda ya zuba kalamai masu ratsa zuciya domin taya matarsa murnar ƙara shekara
  • Chioma Uzodimma ta yi bikin kara shekararta ne ranar Laraba, kuma mijinta ya mata fatan alheri da addu'a

Imo - Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya taya matarsa murna yayin da take bikin ƙara shekara (Birthday) ranar Laraba.

Gwamnan wanda ya tsinci kansa cikin tunawa da soyayyar dake tsakaninsu, ya bayyana matarsa, Chioma Uzodimma, da hasken da ta haskaka rayuwarsa.

Uzodimma ya yi amfani da shafinsa na dandalin sada zumunta Facebook, inda ya saka hotonta tare da zuba kalamai masu ratsa zuciya da kuma yabo bisa goyon bayan da ta jima tana ba shi.

Kara karanta wannan

Bayan ganawa da Buhari, Gwamna Masari ya bayyana mutanen da suka kashe kwamishina a Katsina

Chioma Uzodimma
Gwamna ya shiga shaukin soyayya, ya zuba kalamai masu ratsa zuciya domin taya matarsa murna Hoto: Chioma Uzodimma
Asali: Facebook

Gwamnan Uzodimma yace:

"Tsawon shekarun da suka gabata, ina da dalilin cigaba da miƙa godiya ta ga Ubangiji bisa ni'imar mallaka mun ke, yayan da muka haifa, iyalan gidan mu, mutanen jihar Imo baki ɗaya, da ma mutanen duniya."
"Tun daga rayuwar da muka gina dake a a baya da kuma yanzun da muke jagorantar mutanen jihar Imo, ba ki gaza ba wajen cigaba da goya mun baya da soyayya, kula da kara mun kwarin guiwa, wanda hakan na kara mun karfi."

Wane fata gwamnan ya yi wa matarsa?

Gwamnan ya kuma yi wa matarsa addu'a, wacce take lauya ce kuma wacce ta kirkiri kungiyar taimakon al'umma, gidauniyar Goodhope Flourish.

"Kyakkyawan matata, yayin da kike bikin ƙara shekara, ina rokon Allah mai girma ya cigaba da tallafa miki fiye da tsammani."

Kara karanta wannan

Yadda wani gwamna a Arewa ya kwashi tsabar kudi biliyan N60bn daga lalitar jiharsa, EFCC ta magantu

"Ina fatan duk wata soyayyarsa ta kasance tare da ke, kuma ya cigaba da tallafa miki a kokarin da kike na taimaka wa mutane marasa ƙarfi."
"Ina miƙa sakon taya murna ga hasken da ta haskaka rayuwata. Ina san ki a ko da yaushe."

A wani labarin kuma Bayan ganawa da Buhari, Gwamna Masari ya bayyana mutanen da suka kashe kwamishina a Katsina

Bayan kashe kwamishinan kimiyya da fasaha, Dakta Rabe Nasir, ranar Laraba, gwamnan Katsina , Aminu Masari, yace kisan ba shi da alaƙa da yan bindiga.

Punch ta rahoto gwamnan na cewa ya zama wajibi baki ɗaya jihohin arewa ta yamma su haɗa karfi da ƙarfe wajen magance ƙalubalen tsaro da ya addabi yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel