Yadda PDP da APC suka tashi da Naira biliyan 10 daga kudin saidawa 'yan takara fam

Yadda PDP da APC suka tashi da Naira biliyan 10 daga kudin saidawa 'yan takara fam

  • Fiye da Naira biliyan 10 ake lissafin jam’iyyun PDP da APC sun samu ta harkar saida fam din ‘yan takara
  • A Najeriya saida fam din neman takara a zabe ne hanyar da manyan jam’iyyu suka fi samun kudin-shiga
  • A doka da tsarin mulki, dole ne jam’iyyun siyasa su yi wa INEC bayanin abin da suka tara a shekara

Wani bincike da Daily Trust tayi a makon jiya, ya nuna irin makudan kudin da manyan jam’iyyun siyasar kasar suka tashi da su daga aljihun ‘yan takara.

Da aka yi zaben 2019, asusun jam’iyyun ya kumbura saboda wadanda suka yanki fam din zabe. APC kadai ta samu N7bn daga saida fam a shekarar 2019.

Jam’iyyun su kan yi wa mata rangwame idan za su saye fam domin a rika damawa da su a siyasa.

Kara karanta wannan

Mala Buni na fuskantar barazana, Matasan APC sun nemi kotu ta tsige Shugaban Jam’iyya

APC ta na saida fam din takarar shugaban kasa a kan N45m, na gwamnoni a kan N22.5m, yayin da ake saida na Sanatoci da na Majalisa a kan N7m da N3.85m.

Binciken da jaridar tayi ya nuna APC ta samu N3.59bn daga masu neman zama gwamna, da N3.34bn a hannun wadanda suka saye fam din takarar majalisa.

Yadda PDP ke kamfe
Atiku ya na kamfe a 2019 Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

Buhari ya biya N45m a zaben 2019

Shi kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saye fam dinsa ne a kan N45m. Baya ga haka jam’iyyar APC ta samu N382.5 a zaben gwamnan Edo da Ondo.

Rahoton yace a zabukan cike gurbi da aka shirya a shekarar 2020, jam’iyyar APC mai mulki ta samu kusan N220m, sannan ta sake samun N313m a zabukan 2021.

Kara karanta wannan

Gwamnatin APC ta 'yan koyo ne, mu ne za mu iya gyara Najeriya, inji jam'iyyar PDP

Ita PDP kuwa ta saida fam din takarar shugaban kasa ne a kan N12m, na takarar gwamna ya tashi N6m. Masu neman Sanata da majalisa sun biya N3.5m da N1.5m.

Wadanda suka nemi tikitin takarar shugaban kasa a zaben 2019 sun tarawa PDP N144m. Bayan haka PDP ta samu miliyoyin kudi a hannun sauran ‘yan takararta.

A zaben shugabannin da jam’iyyar PDP ta shirya kwanaki, ta samu N63m. Baya ga N67m da aka samu wajen saida fam ga ‘yan takarar gwamna a Bayelsa da Kogi.

A yammacin ranar Talata ne aka ji cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya zauna da ‘Yan Northern Alliance Committee a birnin tarayya Abuja kan batun zaben 2023.

Bola Tinubu yace ya na shawara da mutanensa a kan tsayawa takarar kujerar shugabancin Najeriya. 'Dan siyasar ya nuna cewa ba zai ba masoyansa kunya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel