Rashin tsaro: Dattawan Katsina sun dura Abuja, sun gana da Shugaba Buhari a fadar Aso Villa

Rashin tsaro: Dattawan Katsina sun dura Abuja, sun gana da Shugaba Buhari a fadar Aso Villa

  • A yau Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya zauna da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a Aso Villa
  • Gwamna Aminu Bello Masari ya jagoranci wasu manyan jihar Katsina zuwa wajen shugaban kasar
  • Mai girma gwamnan ya bayyana halin da ake ciki da irin kokarin da suke yi a kan lamarin tsaro

Abuja - Mai girma Aminu Bello Masari na jihar Katsina, ya yi zama da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Aso Villa a kan batun rashin tsaro.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gwamna Aminu Bello Masari ya zanta da ‘yan jarida bayan zaman sa da shugaban kasar a ranar 14 ga watan Disamba, 2021.

Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya jagoranci tawagar wasu manyan Katsina da suka zanta da Buhari.

Kara karanta wannan

Ku daina sa ran samun wani abin a mulkin Shugaba Buhari – Obasanjo ga mutanen Najeriya

Rahoton yace tawagar ta hada da Sanata Abba Ali, Sanata Mamman A. Danmusa, Alhaji Aliyu Mohammed, Nalado Y, Sarkin Sudan da Alhaji Ahmed Yusuf.

Dole sai jihohi sun hada-kai - Masari

“Abin da ya fi muhimmanci ga jihohi a yaki da ‘yan bindiga, musamman jihohin Arewa maso yamma shi ne mu hada-kai, mu toshe duk wata kafa.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dattawan Katsina
Masari, Buhari da manyan Katsina Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

“Amma idan wata jiha ta na da tsarin da ya ci karo da na wata, shakka-babu, su ('yan bindigan) za su bar wannan jiha, su koma wata jihar.”

- Aminu Bello Masari.

Gwamna Masari ya bayyana cewa an yi dace, jihar Katsina ta na hada-kai da jihohi irinsu Neja da Nasarawa domin ganin an iya shawo kan matsalar tsaro a yankin.

Kisan kwamishinan jihar Katsina

Gwamnan ya yi magana a game da kashe kwamishinansa da aka yi har gida, yace kisan bai da alaka da ‘yan bindiga, yace wasu ne kurum su ka nemi bayansa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari ya nemi duniya tasa Amurkawa a addu'a saboda mutuwar mutane 100

Da yake jawabi a dazu, Masari yace jami’an tsaro za su bankado wadanda suka yi wannan ta’adi.

Sannan gwamnan yace abubuwa sun fara lafawa a jihar Katsina, yace ana ganin cigaba. A cewarsa, ba za a ce komai ya dawo daidai ba, amma da sauki yanzu.

Buhari ya kure adaka - Obasanjo

Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa ‘Yan Najeriya su cire rai Muhammadu Buhari zai yi abin da ya wuce wannan kan batun tsaro.

A wajen wani taro da aka shirya a Abuja, Cif Olusegun Obasanjo yace ayi tunanin Buhari zai iya kara tabuka wani abin da ya wuce wannan, yaudarar kai ne kurum.

Asali: Legit.ng

Online view pixel