Tattalin arzikin Najeriya ya na dab da durkushewa, Sanusi II
- Alhaji Muhammad Sanusi II, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, ya ce tattalin arzikin Najeriya ya na dab da rushewa
- Tsohon sarkin Kano ya tabbatar da cewa kazar da ke saka wa Najeriya kwai ta na dab da shekawa lahira, lamari mara dadi
- Ya yi kira ga gwamnatin da ta rungumi fasahar zamani ta ICT tare da bin turbar da sauran kasashen duniya suke bi
Kaduna - Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Alhaji Muhammad Sanusi, ya ce tattalin arzikin Najeriya ya na dab da rushewa.
A yayin jawabi da yayi na ranar rufe gagarumin taron hannayen jari da aka yi a Kaduna mai taken KadInvest 6.0, Sanusi ya ce baya ga cewa Najeriya ta na da matsala wurin samar da mai, a yanzu kasuwannin duniya ba su siya.
Daily Trust ta wallafa cewa, tsohon sarkin Kanon ya ce "kyakyawar kazar da ke saka wa Najeriya kwai na dab da mutuwa."
Ya ce makomar kasar nan ta dogara ne da tattalin arziki mai dogaro da ilimi, kuma Najeriya an bar ta a baya a cikin kasashen Afrika masu dogaro da kirkire-kirkire.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya jajanta yadda ya kasance kasar Ghana mai karamin tattalin arziki ke zuba hannayen jari a fannin ilimi amma Najeriya ke zuba kashi 7 na kasafinta a ilimi, Daily Trust ta wallafa.
"Mutum takwas kacal a cikin dari na 'yan Najeriya da suka fara karatun firamare ke kammalawa har zuwa jami'a."
"A fadin duniya, aiki ya sauya fasali; kashin talatin zuwa arba'in na ma'aikatan kasashe masu karfin tattalin arziki suna kokarin inganta fasaharsu zuwa 2030. Amma kuma ta yaya ake samun wannan sauyin? Ilimin fasahar sadarwa da kuma aiki daga gida wanda muka gani yayin annobar korona.
“Nan babu dadewa sakako za su koma yin ayyuka a kasashe masu yawa kuma wadanda za su yi aikin za su kasance masu sarrafa sakakon, samar da su ko kuma gyara su.
“A watanni kadan da suka gabata, kasar Jamus ta samar da makamashin da ake sabuntawa domin bukatar dukkan kasar. A yau muna samun matsala wurin siya da man fetur a Najeriya. Ba matsalar samarwa kadai ba, har kasuwa babu.
“Don haka, wannan sauyi ne na dole kuma a matsayin na kasar da ta dogara da man fetur, ya dace abubuwa su sauya."
Ya kara jaddada cewa akwai bukatar kirkirar fasaha domin matasa wanda zai samar da muhallin habakar tattalin arziki da cigaba.
Bidiyon NYSC na shawarta masu hidimar kasa su tattara kudin fansarsu da kansu
A wani labari na daban, a halin yanzu hukumar NYSC ta shiga wani rudani sakamakon wani cece-kuce kan dokokin tsaro da suka bai wa matasa masu hidimar kasa, Daily Trust ta wallafa.
A wani littafi mai suna “Security Awareness and Education Handbook For Corps Members and Staff'” NYSC ta bayyana manyan titunan Abuja zuwa Kaduna, Abuja zuwa Lokoja zuwa Okene da Aba zuwa Fatakwal daga cikin tituna masu tsananin hatsari.
A shafi na 56 na littafin, an shawarci matasa masu kaiwa da kawowa kan wadannan titunan da su sanar da 'yan uwansu tare da samun wanda zai biya kudin fansa matukar aka yi garkuwa da su.
Asali: Legit.ng