NYSC: Masu yi wa kasa hidima da suka yi rigakafin Korona kadai za su shiga sansanin mu

NYSC: Masu yi wa kasa hidima da suka yi rigakafin Korona kadai za su shiga sansanin mu

  • NYSC ta haramta wa duk wasu masu bautar kasa da ke fadin kasar nan da ba su yi riga-kafin COVID-19 ba shiga sansanayenta da ke fadin kasar nan
  • Darekta janar na hukumar, Shuaibu Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin jawabi ga masu bautar kasa na 2021 Batch-C da jami’an sansanayen
  • Ya shaida cewa wajibi ne ko wanne mai bautar kasa ya gabatar da shaidar yin riga-kafin cutar kafin a ba shi damar yin rijistar bautar kasar

Hukumar kula da masu yi wa kasa hidima NYSC ta haramta wa duk wani matashi shiga sansaninta da ke fadin kasar nan matukar bai yi riga-kafin cutar Coronavirus ba, The Guardian ta ruwaito.

Darekta janar na hukumar, Shuaibu Ibrahim ne ya sanar da hakan a wani jawabi da ya yi wa matasan na shekarar 2021 Batch “C” stream Two da kuma jami’an sansanayen.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga daga Zamfara sun kutsa Filato, sun kai farmaki, sun hallaka mutane 10

NYSC: Masu yi wa kasa hidima da suka yi rigakafin Korona kadai za su shiga sansanin mu
Wadanda suka yi rigakafin korona kadai za su shiga sansanin mu, NYSC. Hoto: The Nation
Asali: UGC

Ya ce wajibi ne duk wasu matasan da za su shiga wani sansani su gabatar da shaidar yin riga-kafin cutar Coronavirus kafin a ba su damar yin rijista.

Ya ce an dauki matakin ne don gudun yaduwar cutar

Darekta janar din ya ce hukumar ta na kokarin ganin cutar ba ta yadu ba bayan an gano makamanciyarta, Omicron COVID ta fara yaduwa a kasar.

Ya shaida cewa babu wani hutun makwanni biyu da za a bayar bayan barin sansani don haka ya bukaci matasan su yi kokarin ganin sun koyi sana’o’in hannu don tallafa wa kawanansu.

Ibrahim ya ce matasa su guji tafiyar dare

The Guardian ta shaida yadda Ibrahim ya ja kunnen matasan akan fitar dare da yin tafiye-tafiyen da ba dole ba da dare, inda ya ce ya kamata kada mutum ya kuskura ya kai karfe 6:00pm a kan hanya.

Darekta janar din na NYSC ya ce hukumar ta tanadar wa da masu bautar kasa masauki da wuraren zama cikin barikin sojoji don kwana a jihohi daban-daban idan su ka ga dare ya yi musu don gudun su wuce karfe 6:00pm a kan hanya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel