Jami’ar Masar da kasar UAE sun shiryawa mahaddata gasar karatun Kur’ani a Najeriya

Jami’ar Masar da kasar UAE sun shiryawa mahaddata gasar karatun Kur’ani a Najeriya

  • Jami’ar Al-Azhar Shereef ta Cairo ta shirya gasar karatun littafin Al-kur’ani a birnin tarayya Abuja
  • Wakilan jami’ar da ke Masar sun gudanar da wannan musabaka ne da hadin-kan jakadancin kasar UAE
  • Irinsu Ayman Esmat, Sheikh El-Hasanain El-Moallim da kuma Sheikh AbdelAzeem sun halarci gasar

Abuja - Kwararrun malamai daga jami’ar Al-Azhar Shereef da ke birnin Cairo, kasar Masar sun yi alkawarin cigaba da gudanar da musabaka a Najeriya.

Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 13 ga watan Disamba, 2021, cewa jami’ar ta hada-kai da kasar UAE wajen shirya gasar Al-kur’ani a Abuja.

Wakilan jami’ar ta Al-Azhar Shereef sun bayyana wannan ne a ranar Lahadi, yayin da aka yi bikin rufe gasar da aka shirya na wannan shekarar.

Kara karanta wannan

Kungiyar IZALA ta bada umarnin fara Alkunut a masallatan Ahlissunnah dake fadin Najeriya

An gudanar da wannan gasa ta karatun littafi mai tsarki a cibiyar raye karatun addinin musulunci da ke karkashin masallacin nan na An-Noor.

Manyan fuskoki a wajen gasar

Wadanda suka samu damar halartar musabakar su ne: Darektan Ustadh Abdallah Ahmad bangaren da’awa da yada ilmi na cibiyar addinin musuluncin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Masallaci
Masallacin An Noor Hoto: ICICE Al-Noor Mosque (مسجد النور)
Asali: UGC

Jaridar tace sakataren ofishin jakadancin Masar, Ayman Esmat wanda ya wakilci Jakadan kasar, Sheikh Zakariyya Al-azhari ya na cikin mahalartan gasar.

Imam Tamim Yusuf Alhasan, babban limamin masallacin Juma’a na Zone 3 ya zo wajen musabakar, haka zalika darektan ICICE, Kabir Kabo Usman.

Dalilin kiran irin wannan gasa

Dr. Kabir Kabo Usman a jawabinsa a madadin cibiyar masallacin An – Noor, ya yaba da kokarin da jami’ar take yi wajen bunkasa ilmin musulunci a Najeriya.

Sheikh Assayed El-Hasanain El-Moallim wanda ya shirya wannan musabaka, yace burinsu shi ne yada asalin manufar musulunci, su yaki tsattsauran ra’ayi.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Sarkin Musulmi yace al’umma su rungumi kunutu a masallatai da makarantu

Har ila yau, Sheikh Mahmood AbdelAzeem da yake magana, ya yi bayanin muhimmancin koyon Kur’ani. Za a cigaba da shirya irin wannan gasa a kai-a kai.

Aisha Yesufu ta yi magana

Aisha Yesufu ta fito ta na kokawa cewa a maimakon Jami’an tsaro su kare rayuka da dukuyoyin mutane, su na muzgunawa masu yin zanga-zanga a Arewa.

'Yar gwagwarmayar ta soki masu cewa a dage da addu'a, a guji yin fito na fito da shugabanni, tace hakan ba ya cikin koyarwar Manzon Allah (SAW) a musulunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel