Rashin tsaro: Sarkin Musulmi yace al’umma su rungumi kunutu a masallatai da makarantu

Rashin tsaro: Sarkin Musulmi yace al’umma su rungumi kunutu a masallatai da makarantu

  • Sarkin Musulmi ya bada shawara ga al’ummar musulmai su dage da yawaita addu’o’i na musamman
  • Muhammad Sa'ad Abubakar III ya yi wannan kira ne ta bakin kungiyar Jama'atu Nasril Islam a makon jiya
  • Mai alfarma Sultan yace hakan ya zama dole ne duba da irin halin rashin tsaron da ake fama da shi a yau

Sokoto - Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya yi kira ga al’umma da su dage da yin addu’o’i na musamman a kan batun rashin tsaro.

Muhammad Sa'ad Abubakar III ya bukaci a dage da yin adduo’in al-kunutu, ganin halin da aka shiga a kasar nan. BBC Hausa ta fitar da wannan rahoton.

Sarkin Musulmi ya na so a rika yin wadannan addu’o’i a duk wasu masallatai da dakunan ibada da wuraren zama domin Allah ya kawowa al’umma sauki.

Kara karanta wannan

Kasashen musulman duniya sun yi Allah-wadai da babbaka matafiya a Sokoto

Sakataren kungiyar JNI, Dr. Khalid Abubakar Aliyu ya fitar da jawabin da Sarkin Musulmin ya yi.

Mai alfarma Muhammad Sa’ad III shi ne yake jagorantar mafi kololuwar majalisar addinin musulunci a kasar nan, ƙungiyar Jama'atu Nasril Islam (JNI).

Sarkin Musulmi
Sarkin Musulmin Najeriya Hoto: www.wilsoncenter.org
Asali: UGC

Wata sanarwa daga ƙungiyar Jama'atu Nasril Islam (JNI) wadda sarkin Musulmi ke jagoranta ta ce an yi kiran ne saboda ya zama dole a irin wannan yanayi.

"Wannan kiran ya zama dole idan aka duba yadda ake ci gaba da kashe rayuka da wulaƙanta su gabagaɗi kamar yadda muka gani a Sokoto da Gidan Bawa da Beni-sheikh da Kaga."
"Saboda haka ana kiran Musulmi su duƙufa wajen yin alƙunutu a raka'ar ƙarshe ta dukkan sallolin farilla da na nafila domin neman taimakon Allah."

- Dr. Khalid Abubakar Aliyu.

Kara karanta wannan

Tsaro: Kungiyar Izala ta yi kira da Buhari ya tashi tsaye, jama’a kuma su dage da addu'a

Har ila yau, BBC Hausa ta rahoto JNI a madadin Sultan yana bada shawarar mutane su hada da yawan yin zikiri, addu'o'i a kowace sujada da yawaita addu’a.

Sa’ad III ya bukaci a rika addu’o’in a masallatai da makarantun allo da sauran wuraren karatu.

Halin da ake ciki ya tabarbare

Alƙalumma sun nuna cewa mutum 363 aka sace a Najeriya a watan Nuwamban da ya wuce.

A 'yan kwanakin nan an ji yadda wasu miyagun 'yan bindiga suka tare mota a Sokoto, suka banka mata wuta. Duniya tayi Allah-wadai da wannan ta'asa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel