Gobara ta kama dakin kwanan dalibai a jami'ar Taraba, daliba ta kone kurmus

Gobara ta kama dakin kwanan dalibai a jami'ar Taraba, daliba ta kone kurmus

  • Wata gobara ta kama a jihar Taraba, inda ta hallaka wata daliba da cikin dakin kwanan dalibai na jami'ar Taraba
  • Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa, hakan ya faru da daren Juma 10 ga watan Disamba
  • An ruwaito cewa, gobarar ta fara ne yayin da wani soket a dakin ya kone, ya kuma kama katifa har ya kai kone dalibar

Taraba - Wata dalibar aji daya a Jami’ar Jihar Taraba (TSU) ta mutu sakamakon gobarar da ta tashi a dakin kwanan daliban.

A cewar gidan talabijin na Channels, dalibar mai suna Enuseh Lawi ta makale ne yayin gobarar a daren Juma’a.

An tattaro cewa gobarar ta taba wasu sassa na Zenith Hostel da Enuseh ta ke zaune har ta mutu.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari hazikar dalibata ce a darasin Physics, Malamar uwargidan shugaban kasa

Kofar jami'ar jihar Taraba
Gobara ta kama dakin kwanan dalibai a jami'ar Taraba, daliba ta kone kurmus | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

An ce gobarar ta tashi ne yayin da dalibar ke kwance tana bacci, TheCable ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An ruwaito daga majiyoyin da ke da masaniya kan lamarin na cewa wasu dalibai mata suka balla dakin kafin a samu damar shiga.

An ce an garzaya da ita asibitin kwararru na Jalingo inda aka ce ta rasu.

Gobarar da ta shafi wasu sassa na dakin kwanan dalibai, ta jawo asarar dukiya da sauran kayayyaki masu daraja.

A cewar majiyar:

“An gaya mini cewa dalibar ta tafi karatu da dare saboda jarrabawarta kuma ta dawo a gajiye, don haka ta yi barci.
“Musabbabin wannan gobarar ta samo asali ne daga wani soket na wutan lantarki wanda ya kone kuma ba zato ba tsammani ya kama katifar da ke kusa da ita inda ta bazu ko’ina."

Kara karanta wannan

Rahoton ‘yan sanda: Dalibai biyu sun mutu, 12 sun jikkata a hatsarin babbar mota ranar Talata

Innalillahi: Basaraken gargajiya a Ogbomoso ya riga mu gidan gaskiya

A wani labarin na daban, basaraken garjiya mai sarautar Soun na Ogbomoso, Oba Oladunni Oyewumi, Ajagungbade III, ya rasu.

Majiyoyi na kusa da sarkin a fadar sun shaida wa wakilin jaridar Punch cewa, basaraken mai shekaru 95 ya rasu ne da safiyar yau Lahadi.

Wasu majiyoyi guda biyu ne suka tabbatar da hakan a garin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel