Innalillahi: Basaraken gargajiya a Ogbomoso ya riga mu gidan gaskiya

Innalillahi: Basaraken gargajiya a Ogbomoso ya riga mu gidan gaskiya

  • Basaraken gargajiya a Ogbomoso ya riga mu gidan gaskiya da safiyar yau Lahadi 12 ga watan Disamba
  • Majiyoyi daga fadar Ogbomoso ta bayyana haka ne, duk da cewa ba a sanar da hakan a hukumance ba
  • An haife shi a ranar 27 ga Mayu, 1926, ya kuma hau kan karagar mulki a ranar 24 ga Oktoba, 1973

Oyo - Basaraken garjiya mai sarautar Soun na Ogbomoso, Oba Oladunni Oyewumi, Ajagungbade III, ya rasu.

Majiyoyi na kusa da sarkin a fadar sun shaida wa wakilin jaridar Punch cewa, basaraken mai shekaru 95 ya rasu ne da safiyar yau Lahadi.

Wasu majiyoyi guda biyu ne suka tabbatar da hakan a garin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Basaraken gargajiya a Ogbomoso, Oba Oladunni Oyewumi
Innalillahi: Basaraken gargajiya a Ogbomoso ya riga mu gidan gaskiya | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A cewar majiyar:

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Sojoji sun cafke Shugaban ‘Yan banga bisa zargin alaka da ‘Yan bindiga

“Gaskiya ne Baba ya rasu. Hakan ya faru da safiyar yau amma ba a sanar da hakan a hukumance ba.
“Ya yi rayuwa mai kyau kuma ya bar suna mai kyau da yawa. Nan ba da jimawa ba fadar za ta sanar da hakan.”

An haife shi a ranar 27 ga Mayu, 1926, a Ogbomoso kuma da ne ga Oba Bello Afolabi Oyewumi Ajagungbade II da Olori Seliat Olatundun Oyewumi.

Oba Oyewumi ya hau karagar mulki ne a ranar 24 ga Oktoba, 1973.

Fitaccen dan kasuwa, Alhaji Sani Buhari, ya riga mu gidan gaskiya

A wani labarin, hamshaki kuma gawurtaccen dan kasuwa Alhaji Sani Buhari Daura ya riga mu gidan gaskiya, Daily Trust ta ruwaito.

Rahoto daga majiya ya tattaro cewa hamshakin dan kasuwar ya rasu ne a Dubai da sanyin safiyar yau Lahadi.

Kara karanta wannan

Tsaro: Ko tausayi ba ka bani, kai kace sai kayi Shugabancin kasa: Akande ya fadawa Buhari a gabansa

Ya rasu yana da shekaru 89 a duniya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel