Sarki ya tube rawanin jigon jam'iyyar APC saboda ya caccaki gwamnan da ya bashi kyautar Mota

Sarki ya tube rawanin jigon jam'iyyar APC saboda ya caccaki gwamnan da ya bashi kyautar Mota

  • Gwamnatin jihar Adamawa ta baiwa sarakunan jihar kyautar motoci biyu kowannen su
  • Lamidon Adamawa, Alhaji Muhammadu Barkindo, ya tube rawanin jigon APC a jihar saboda ya caccaki gwamna kan kyautar
  • Yace Umar Mustapha, wanda tsohon ɗan takarar gwamna ne, bai dace da rike sarautar ba

Adamawa - Sarkin Adamawa, wanda aka fi sani da lamidon Adamawa, Muhammadu Barkindo, ya kwace rawanin da ya naɗa wa Umar Mustapha saboda ya caccaki gwamna Ahmadu Fintiri.

Premium Times ta rahoto cewa jigo a jam'iyyar APC ya caccaki gwamnan Adamawa ne bayan ya baiwa sarakunan gargajiya sabbbin motoci.

Masarautar Adamawa ta bayyana cewa Umar Mustapha bai cancanci ya cigaba da rike mukamin, 'Mukaddas Adamawa’.

Lamidon Adamawa
Sarki ya tube rawanin jigon jam'iyyar APC saboda ya caccaki gwamnan da ya bashi kyautar Mota Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Mista Mustapha, tsohon ɗan takatar gwamnan jihar Adamawa karkashin APC, a wata sanarwa da ya fitar, ya caccakin gwamnan kan kyautar.

Yace:

"Bai kamata a kashe miliyan N200m wajen siyo sabbin motoci ga sarakuna ba yayin da masu jiran Fansho ke mutuwa sanadiyyar yunwa."

Tsohon ɗan takaran ya yi wannan furucin ne bayan gwamnatin Adamawa ta mika wannan abun alheri ga sarakunan.

Wane mataki masarauta ta ɗauka?

Bayan haka ne sarki Barkindo, a wata sanarwa ta hannun sakataren masarauta, Khalil Kawu, yace an tube rawanin Mista Mustapha.

Wani sashin sanarwan masarautar yace:

"Mai martaba sarki ya bayyana cewa Umar Mustapha bai cancanci rike mukamin sarauta ba sakamakon caccakar da ya yi wa gwamna kan motocin da aka baiwa sarakuna a jihar."

Sarkin ya kuma nuna tsantsar damuwarsa kan cewa Mustapha ya gaza fahimtar kyakyawan kudirin da gwamnati ta yi wa Sarakunan gargajiya wannan kyauta.

Kyautar motoci ga sarakuna

A ranar 1 ga watan Disamba, gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya sanar da bada kyautar motoci ga sarakunan jihar Adamawa a gidan gwamnatinsa dake Yola.

Kakakin gwamnan, Muhammadu Tukur, yace sarakunan, waɗan da suka halarci taron da suka saba yi da gwamna a gidan gwamnati, kowanen su ya karbi motar Hulux da SUV.

Ya kuma bayyana cewa gwamna ya ƙara gode wa sarakunan bisa taka rawar da suke wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Yace gwamnati ta ɗauki matakin basu kyautar motocin ne domin saukake musu ayyukan da suke na ƙara gina zaman lafiya.

A wani labarin kuma Hukumar EFCC ta gano wani gwamnan Arewa da ya wawuri tsabar kudi biliyan N60bn daga lalitar jiharsa

Hukumar EFCC tace sabon sashin da ta kirkiro na fasaha ya fara aiki, domin zuwa yanzun ya gano wasu bayanan sirri.

Hukumar tace ɗaya daga cikin abubuwan da sashin ya bankado shine yadda wani gwamna ya cire kudi daga lalitar jiharsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel