Ana shirin ruguza gidajen mutane 1000 domin gwamnatin Legas ta gina titin jirgin kasa
- Hukumar LAMATA ta sanar da mutane cewa kowa ya tashi daga yankin Itoki-Agbado-Ijoko a Ifo
- Gwamnatin Legas za ta gina jirgin kasa da zai rika daukar fasinjoji don haka za a rusa gidajen jama'a
- Itoki-Agbado-Ijoko na cikin wuraren da za a ruguza domin a samu hanyar da jirgin kasa zai wuce
Lagos - Gwamnatocin Legas da Ogun za su samu sabani a dalilin sanarwar da aka ba jama’a na cewa su tashi daga yankin Itoki-Agbado-Ijoko a jihar Ogun.
Daily Trust tace gwamnatin jihar Legas ta hannun hukumar LAMATA, ta bukaci mutane da ‘yan kasuwa su bar Itoki-Agbado-Ijoko a karamar hukumar Ifo.
Hukumar LAMATA mai kula da harkar sufuri a jihar Legas ta na so wadannan mutane da ke kan iyaka tsakaninta da Ogun su tashi domin a gina titin jirgi.
Rahoton yace yankunan Itoki-Agbado-Ijoko da ke jihar Ogun, duk su na cikin wuraren da titin jirgin kasan da gwamnatin Legas ta ke shirin ginawa zai bi.
Tun a farkon Nuwamba, jami’an LAMATA su ka aika takarda su na sanar da jama’a cewa su cire kayansu daga Itoki-Agbado-Ijoko saboda aikin dogon da za ayi.

Asali: UGC
LAMATA ta fitar da takarda da taken: “Lagos Rail Mass Transit Red Line Project Development: Removal Notice On Physical Development Within The Right of Way.”
Majalisar jihar Ogun ta sa baki
Jaridar Daily Post tace gidaje kimanin 1, 000 wannan aiki da gwamnatin Legas ta dauko zai shafa.
Jami’an hukumar LAMATA sun tuntubi ma’aikatar sufuri ta jihar Ogun a game da wannan lamari, amma ‘yan majalisar dokoki na Ogun sun ce ba za ta sabu ba.

Kara karanta wannan
Hukumar jami'a ta kori lakcarorinta 4 bisa karbar kudi ta bayan fage da rashin da'a
A zamansu na ranar Alhamis, ‘Yan majalisan sun yi watsi da sanarwar da gwamnatin Legas ta fitar, suka ce ba zai yiwu a rusa gidajen mutane haka kurum ba.
Shugaban majalisar dokoki, Rt. Hon. Olakunle Oluomo ya bukaci a fito da yarjejeniyar fahimta ta MoU tsakanin jihohin biyu kafin LAMATA ta fara rushe-rushen.
Littafin tarihin Bisi Akande ya fito
A littafin da ya rubuta, tsohon Gwamnan Osun kuma shugaban APC na farko, Cif Bisi Akande yace Olusegun Obasanjo ba wani mutumin da za yarda da shi ba ne.
Bisi Akande ya yi wa Obasanjo kaca-kaca, yace bai da amana da alkibla, ya na gantali a siyasa. Akande ya bayyana haka ne da ya tabo batun Marigayi Bola Ige.
Asali: Legit.ng