Sojoji Sun Kashe 'Yan Ta'adda 62, Wasu 192 Sun Miƙa Wuya, Hedkwatar Tsaro

Sojoji Sun Kashe 'Yan Ta'adda 62, Wasu 192 Sun Miƙa Wuya, Hedkwatar Tsaro

  • A ranar Alhamis Hedkwatar Tsaro ta ce Rundunar Sojin Najeriya ta halaka fiye da ‘yan bindiga 62 a yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya cikin makwanni biyu
  • Sannan cikin tarin nasarorin da aka samu har ‘yan ta’adda 192 ne su ka zubar da makamansu a cikin wannan datsin, cikinsu kuwa har da yara 74
  • Mukaddashin darektan watsa labaran soji, Birgediya janar Bernard Onyeuko ne ya sanar da hakan inda ya ce lamarin ya faru ne tsakanin 25 ga watan Nuwamba zuwa 9 ga watan Disamba

Abuja - A ranar Alhamis, Hedkwatar Tsaro ta shaida yadda rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar halaka fiye da ‘yan ta’adda 72 a yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya cikin makwanni biyu.

Ta shaida yadda ‘yan ta’adda 192 ciki har da yara su ka zubar da makamansu a cikin datsin nan kamar yadda ta wallafa a shafinta na Facebook.

Kara karanta wannan

Babbar magana: 'Yan sanda sun shiga damuwa bayan jin shuru na albashin Nuwamba

'Yan Ta'adda 192 Ciki Har da Yara Sun Mika Wuya Cikin Makonni 2, Hedkwatar Tsaro
Hedkwatan Tsaron Najeriya ta ce 'yan ta'adda 192 sun mika wuya cikin makonni biyu. Hoto: DHQ
Asali: Facebook

Mukaddashin Darekta Watsa Labaran Soji, Birgediya janar Bernard Onyeuko ya ce tsakanin ranar 25 ga watan Nuwamba zuwa 9 ga watan Disamba ‘yan ta’addan su ka zubar da makamansu.

Cikinsu har da yara 74

Ya kara da cewa cikinsu akwai maza manya 51, mata 67 da kuma kananun yara 74.

Sanarwar ta bayyana yadda ya ce sun zubar da makamansu ga sojoji ne a karamar hukumar Gombi, a kauyakun Rann/Rumirgo da Biu, Bama, Mafa da karamar hukumar Dikwa.

Ya ce an mika wadanda su ka zubar da makaman na su gaban hukumomin da su ka dace don a dauki matakan da suka dace.

Onyeuko ya ce cikin kwanakin nan an kama ‘yan ta’adda 28 sannan an kwace miyagun makamai 54 da wasu iri daban-daban daga wurinsu.

Kara karanta wannan

Rahoton ‘yan sanda: Dalibai biyu sun mutu, 12 sun jikkata a hatsarin babbar mota ranar Talata

Har dabbobi aka amshe a hannunsu

Kamar yadda ya shaida:

“Sojoji sun samu dabbobi 101 da ake zargin sun kwace daga hannunsu sannan an ceto ‘yan sanda 20 da su ka sace a ofishin ‘yan sandan Buni Yadi.”

Har ila yau a ranar 3 ga watan Disamba Operation Hadarin Daji su ka yi musayar wuta da mayakan Boko Haram da ISWAP a karamar hukumar Kala Balge.

Yayin turnukun, sojoji sun halaka fiye da ‘yan ta’adda 26 sannan sun samu nasarar lalata sansanayensu da ababen hawansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel