Kano: An gano sababbin gawawwakin ‘Yan makarantan da ruwa ya ci a kauyen Bagwai

Kano: An gano sababbin gawawwakin ‘Yan makarantan da ruwa ya ci a kauyen Bagwai

  • Mutane sun kuma gano gawawwakin ragowar wasu Bayin Allah da suka mutu a kauyen Bagwai
  • Wadannan ‘yan makaranta sun mutu ne a sanadiyyar mummunan hadarin jirgin ruwa kwanaki
  • Adadin wadanda suka yi shahada a hanyarsu ta zuwa Bagwai daga kauyen Badau sun haura 40 a yanzu

Kano - An ga gawawwakin mutane 13 da ba a san inda suke ba tun bayan hadarin jirgin ruwan da ya auku a wani kauye a garin Bagwai, jihar Kano.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 6 ga watan Disamba, 2021, cewa an gano gawar mutane 13 da suke nutse a hadarin ruwa.

Hakan ya na nufin adadin mutanen da ruwan ya ci a mummunan hadarin da aka yi ya kai 42.

Babu mamaki a safiyar ranar Talata ayi jana’izar wadanda suka riga mu gidan gaskiya a kauyen Badau, kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Kara karanta wannan

Jihar Niger: 'Yan bindiga na karbar sigari da wiwi a matsayin kudin fansa

Gwamnan Kano
Gwamnan Kano Ganduje Hoto: @Dawisu
Asali: Twitter

Yadda abin ya auku

Idan ba a manta ba, jirgin ruwa ya kife da mutane kusan 50 da suka taso daga makarantar Madinatul Islamiyya daga wani kauye, za su je Bagwai

Wadannan yaran makaranta sun taso ne daga bikin Mauludin Annabi Muhammadu (SAW). Ba wannan ne karon farko da jirgi ya kifi a wannan ruwa ba.

An gano gawar mutane 29, daga ciki an tabbatar da cewa an ceci mutane bakwai da suka yi rai.

Kokarin da gwamnati tayi

Rahoton yace gwamnatin jihar Kano ta kafa wani kwamiti na musamman da zai binciki abin da ya jawo wannan hadari da ya yi sanadiyyar rayuwa.

Baya ga haka, Mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya raba motoci biyu da za su rika safarar fasinjoji daga kauyen Badau zuwa garin Bagwai.

Kara karanta wannan

Hatsarin jirgin ruwa a Kano: Adadin mutanen da suka mutu a hatsarin ya ƙaru zuwa 29

Sannan gwamnati ta raba buhunan masara da shinkafa da kuma sukari da gishi ga wadanda abin ya shafa, baya ga gudumuwar kudi Naira miliyan shida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel