Lauya ya kai karar Shugaban kasa da Ministocinsa kotu a kan nade-naden mukamai a FCTA

Lauya ya kai karar Shugaban kasa da Ministocinsa kotu a kan nade-naden mukamai a FCTA

  • Maxwell Opara ya yi karar shugaba Muhammadu Buhari a dalilin mukaman da aka bada a FCTA
  • Lauyan da yake kare hakkin Bil Adama yace ba ayi wa mutanen Kudu adalci a rabon kujerun ba
  • Sauran wadanda ake kara a kotun da ke Abuja sun hada da Ministocin shari’a da na birnin tarayya

FCT, Abuja - Wani lauya mai kare hakkin Bil Adama a birnin tarayya Abuja, Maxwell Opara, ya shigar da karar shugaban kasa Muhammadu Buhari a kotu.

Vanguard ta ce Barista Maxwell Opara ya na zargin Mai girma Muhammadu Buhari da saba dokar daidaiton rabon mukamai a nade-naden da aka yi a FCTA.

Wannan lauya da ya shigar da kara a babban kotun tarayya da ke zama a Abuja, yace mukaman da aka nada kwanan nan a hukumar FCTA sun sabawa doka.

Kara karanta wannan

An gano abin da Buhari ya fadawa Shugaban kasar Afrika ta Kudu kafin ya lula zuwa Dubai

Hakan na zuwa ne bayan an nada sababbin sakatarorin din-din-din, manyan sakatarori, hadimai da kuma darektoci da hukumar mai kula da birnin tarayya Abuja.

Maxwell Opara yace an zakulo wadanda aka ba mukaman ne daga yankin Arewacin Najeriya.

Lauya ya kai karar Shugaban kasa
Buhari a Dubai EXPO Hoto: @femi.adesina
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauran wadanda ake kara

Baya ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, Maxwell Opara ya na kuma tuhumar Ministan birnin tarayya, Malam Mohammed Musa Bello a gaban Alkali.

Jaridar tace sauran wadanda ake kara su ne AGF, Ministan shari’a na kasa, Abubakar Malami da hukumar FCC mai daidaita rabon kujeru da mukamai a kasa.

Lauyan da ya yi suna wajen kare hakkin jama'a ya nemi kotu ta bukaci wadanda ake kara, su bi sashe na 4 da na 5 na dokar FCC wajen nadin mukamai a FCTA.

A dogon korafin na sa Opara ya fadawa Alkali cewa Mohammed Musa Bello da sauran wadanda ake zargi da laifi sun nada mukamai ba tare da bin ka’idoji ba.

Kara karanta wannan

Sanusi: Gwamnati ta bayyana mataki na gaba bayan tsohon Sarki ya yi nasara a kan ta a kotu

Lauyan yace mafi yawan wadanda suka samu mukamai sun fito ne da jihohin Arewacin kasa. Rahoton yace har zuwa yanzu ba a sa ranar da za a fara shari'a ba.

Ramaphosa ya ziyarci Najeriya

A shekaran jiya ne aka yi wata ganawa ta musamman tsakanin Mai girma Muhammadu Buhari da Shugaban kasar Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa a Aso Villa.

Najeriya ta jaddada muhimmancin samun hadin-kai tsakaninta da Afrika ta Kudu a wajen wannan taro da Buhari ya halarta kafin ya wuce zuwa kasar UAE.

Asali: Legit.ng

Online view pixel