Litar fetur zai zarce N340 a farkon shekarar 2022 idan gwamnati ta cire tallafi inji ‘Yan kasuwa

Litar fetur zai zarce N340 a farkon shekarar 2022 idan gwamnati ta cire tallafi inji ‘Yan kasuwa

  • Shugaban NNPC, Mele Kolo Kyari, yace za a janye tallafin mai don haka fetur zai kai N320 zuwa N340
  • ‘Yan kasuwa sun bayyana cewa idan gwamnatin tarayya ta daina biyan tallafi, farashin zai haura haka
  • Za a samu karin fiye da 100% a dalilin wahalar Dalar Amurka da ake yin ciniki da ita a kasashen waje

Jaridar Punch ta rahoto cewa farashin litar man fetur zai yi mummunan tashi a shekara mai zuwa idan gwamnatin tarayya ta janye tallafin da ta ke biya.

A makon da ya gabata ne shugaban NNPC na kasa, Mele Kyari, ya bada sanarwar za a daina biyan tallafi wanda hakan zai sa man fetur ya kai N320 zuwa N340.

Lissafin da ake yi shi ne babu tabbacin farashin zai tsaya a N340 idan ‘yan kasuwa sun koma harkar.

Kara karanta wannan

Yadda Buhari ya yi wa Jonathan da PDP adawa a kan cire tallafin fetur kafin ya hau mulki

Ana tunanin farashin kowane litar fetur ya kai sama da N340 a watan Fubrairun 2022. Wannan har ya zarce hasashen da kamfanin mai na NNPC yake yi.

'Yan kasuwa za su koma shigo da PMS

Haka zalika rahoton ya bayyana cewa manya da sauran ‘yan kasuwa masu zaman kansu, sun shirya cigaba da shigo da man fetur da zarar an cire tallafin mai.

Sai dai ‘yan kasuwan na tsoron yadda za a yi fama da tashin farashin kaya da karancin Dala, wanda wadannan za su yi tasiri kan yadda za a rika saida man.

Litar fetur
Gidan mai a Najeriya Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

Farashin Dala, farashin fetur

An shafe shekaru kusan hudu, kamfanin NNPC kadai yake shigo da fetur. Hakan ya bayu ne ga wasu dalilai, daga ciki shi ne samun Dalar Amurka ya yi wuya.

Kara karanta wannan

Muna goyon bayan kara farashin man fetur dari bisa dari, Yan kasuwan Mai IPMAN

A halin yanzu gwamnati ta ce a saida fetur a gidajen mai tsakanin N162 zuwa N165. Amma a wasu wuraren, lita ta kai N180 saboda wahalar man da ake yi.

‘Yan kasuwa sun shaidawa manema labarai cewa farashin lita ba zai tsaya a N320 ko N340 da NNPC ke cewa ba, muddin aka cigaba da wahalar samun Dala.

Masu jigilar fetur a karkashin kungiyoyin IPMAN da PETROAN sun ce sun shirya cigaba da shigo da fetur, amma za a ga tsada sosai a shekarar 2022 da za a shiga.

Ukadike Chinedu wanda shi ne shugaban kungiyar IPMAN yace Dala ne zai tsaida farashi. Shi ma shugaban PETROAN Billy Gillis-Harry, ya tabbatar da wannan.

Buhari da tallafin fetur

A makon nan kun ji yadda a shekarun baya Janar Muhammadu Buhari ya ke cikin masu yaki a kan janye tallafin man fetur, har a lokacin da yake mulkin soja.

Amma sai ga shi bayan hawan sa mulki a Mayun 2015, shugaba Buhari ya koma goyon bayan cire tallafin mai, ya kuma kara farashin man fetur kusan sau hudu.

Kara karanta wannan

Cire tallafin mai da biyan N5,000: Sai ka rasa wanda ke ba Gwamnatin nan shawara, Dr Ahmed Adamu

Asali: Legit.ng

Online view pixel