Gwamna Zulum ya ɗauki nauyin marayu 500 na yan sakai da suka rasa ransu a yaƙi da Boko Haram

Gwamna Zulum ya ɗauki nauyin marayu 500 na yan sakai da suka rasa ransu a yaƙi da Boko Haram

  • Gwamna Zulum na jihar Borno zai ɗauki nauyin karatun marayu da iyayen su mata na yan sa'kai da suka mutu a yaki da Boko Haram
  • Zulum yace waɗan nan marayu da iyayen su mata zasu shiga sabon tsarin da gwamnatin Borno zata kaddamar a 2022
  • Gwamnan yace gwamnatinsa ta shirya domin tallafa wa iyalan waɗan nan jami'ai da abubuwan more rayuwa

Borno - Gwamnatin jihar Borno ta sanar da cewa zata ɗauki nauyin marayu 500 na jami'an sakai (CJTF) waɗan da suka mutu a wurin yaƙi da Boko Haram.

Gwamnan jihar, Babagana Zulum, shine ya sanar da shirin gwamnatin ranar Talata, yayin da yake gabatar da kasafin kudin 2022 ga majalisar dokokin jihar Borno.

A wani rubutu da gwamnan ya yi a shafinsa na Facebook, yace an kirkiri jami'an CJTF na yan sa'kai domin su taimakawa sojojin Najeriya wajen yaƙi da yan ta'addan Boko Haram.

Gwamna Zulum
Gwamna Zulum ya ɗauki nauyin marayu 500 na yan sakai da suka rasa ransu a yaƙi da Boko Haram Hoto: The Governor Of Borno State
Asali: Facebook

Mafi yawan mayakan, da suka haɗa da mafarauta, da yan bijilanti na kungiyar CJTF sun rasa rayuwarsu ne yayin yaƙi domin dawo da zaman lafiya a jihar.

Wane shirin gwamnati ke wa iyalansu?

A cewar Zulum, gwamnatin jihar Borno zata girmama ƴaƴan waɗan nan jami'an a matsayin, "Gwarazan jihar Borno."

Yace gwamnatinsa zata kaddamar da shirin tallafawa gwarazan Borno a shekarar 2022 kuma zata taimaki matan da suka bari da kayan more rayuwa.

Zulum yace:

"A watan Janairu 2022 gwamnati zata kaddamar da shiri mai taken, 'Borno Heroes Support Programme’ wanda zai ɗauki nauyin karatun marayu 500 da iyayensu mata, waɗan da mambobin kungiyoyin sa'kai suka mutu suka bari."
"Mun yi shirin kaddamar da wannan tsari, kuma zamu naɗa kwamiti da zai tantace marayun da suka kai matakin Firamare ko Sakandire, waɗan da iyayen su suka mutu a yaki da Boko Haram."

"Zamu ɗauki nauyin karatun waɗan nan marayu a makarantun gwamnati da ma makarantun ƙasa-da-ƙasa. Tsarin zai tafi rukuni-rukuni, a wannan rukunin zamu ɗauki mutum 500."

Cikin kwana 30 zamu gyara wutar lantarki a Maiduguri - Zulum

A wani labarin na daban kuma Zulum yace gwamnatinsa zata gyara hasken wutar lanyarkin Maiduguri da kewaye

Gwamna Babagana Umaru Zulum na jihar Borno, ya sha alawashin yin duk me yuwu wa wajen dawo da hasken wutar lantarki Maiduguri.

Zulum ya bayyana cewa idan Allah ya yarda nan da kwana 30 kacal wuta zata koma kamar da a babban birnin da kewayensa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel