Da duminsa: Hukumar EFCC ta sake Femi Fani-Kayode, bayan tasa keyarsa a kotu

Da duminsa: Hukumar EFCC ta sake Femi Fani-Kayode, bayan tasa keyarsa a kotu

  • Bayan kwashe sa'o'i hannun jami'an hukumar EFCC, Fani Kayode za kwana gidansa da daren nan
  • Hukumar na tuhumar tsohon ministan sufurin jiragen saman ne kan wasu takardun bogi da ya gabatar
  • Tun bayan zaben 2015 hukumar ta gurfanar da Kayode kan almundahanan wasu kudade

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ya saki tsohon ministan sufuri, Femi Fani Kayode, rahoton TVC News.

Hukumar ta bashi beli bayan sa'o'in da ya kwashe a ofishinta na Legas.

Mun kawo muku rahoton cewa EFCC ta damke shi a wata babbar kotun tarayya ce da ke zama a Ikoyi, jihar Legas kuma an tafi da shi ofishin hukumar EFCC mafi kusa.

Tsohon ministan, wanda aka gurfanar a gaban kotu kan takardun bogi, ya na kokarin fita daga kotun ne bayan an dage shari'ar zuwa ranar 24 ga watan Janairun shekara mai zuwa, yayin da mai binciken EFCC ya dumfare sa.

Kara karanta wannan

Da duminsa: An damke Fani-Kayode a kotun Legas, EFCC ta tafi da shi da shi ofishin ta

Da duminsa: Hukumar EFCC ta sake Femi Fani-Kayode, bayan tasa keyarsa a kotu
Da duminsa: Hukumar EFCC ta sake Femi Fani-Kayode, bayan tasa keyarsa a kotu
Asali: Original

Laifin me yayi?

Mai binciken na hukumar EFCC, Shehu Shuaibu, ya ce ana tuhumar tsohon ministan sufurin jiragen saman ne kan wasu takardun bogi.

Hukumar yaki da rashawan ta shirya tuhuma kan zargi 17 na halasta kudin haram da suka kai N4.6 biliyan kan Fani-Kayode tare da tsohon karamin ministan kudi, Nenandi Usman.

A tare da wadanda ake zargin akwai Yusuf Danjuma, tsohon shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi da kamfanin Jointrust Dimentions Nigeria Ltd.

Wanda ake zargin ya gurfana a gaban Mai shari'a Mohammed Aikawa na babbar kotun tarayya da ke Legas, kuma ya musanta aikata dukkan laifukan sannan an bayar da belinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel