Da Ɗumi-Ɗumi: Matar Sarkin Ningi ta riga mu gidan gaskiya

Da Ɗumi-Ɗumi: Matar Sarkin Ningi ta riga mu gidan gaskiya

  • Matar Mai Martaba Sarkin Ningi, Hajiya Hama Danyaya ta riga mu gidan gaskiya
  • Masarautar Ningi, a ranar Talata, ta tabbatarwa menema labarai rasuwarta a ranar Talata
  • Marigayiyar ta rasu ta bar 'ya'ya takwas cikinsu har da Ciroman Ningi, Haruna Yunusa da Damburam Ningi, Yusuf Yunusa

Jihar Bauchi - Hajiya Hajima Hama Danyaya, matar mai martaba sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya ta riga mu gidan gaskiya.

Ta rasu ne a ranar Litinin da rana, tana da shekaru 85 a duniya.

Masarautar Ningi ta tabbatar wa manema labarai rasuwarta cikin wata sanarwa da ta fitar, Daily Trust ta ruwaito.

Labari Da Duminsa: Allah ya yi wa matar Sarkin Ningi rasuwa
Hajiya Hajima Hama Danyaya, matar Sarkin Ningi ta rasu. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Diyar Gwamnan jihar Kano ta zama Malamar addini, ta na zuba wa’azi da ayoyin Kur’ani

Sanarwar ta ce, marigayiyar, wacce ta auri Alhaji Danyaya a shekarar 1952, ta rasu ta bar 'ya'ya takwas, cikinsu har da Ciroman Ningi, Alhaji Haruna Yunusa da Damburam Ningi, Alhaji Yusuf Yunusa.

Sanarwar ta ce:

“Innalillahi Wa Inna Ilaihim Rajiun! Muna sanar da rasuwar Hajima Hama Yunusa Danyaya, matar mai Marta Sarkin Ningi, Alhaji (Dr) Muhammad Yunusa Danyaya."

Sanarwar ta kara da cewa an yi mata jana'iza a safiyar ranar Talata bisa koyarwar addinin musulunci.

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel