Yadda buga cacar wasanni ke mamaye zukatan yan Najeriya da cinye tattalin arzikinsu

Yadda buga cacar wasanni ke mamaye zukatan yan Najeriya da cinye tattalin arzikinsu

  • Wasan caca a Najeriya ya zama ruwan dare ga matasa har da manyan mutane musamman mabiyan addinin kirista da musulunci
  • Ra'ayoyin da muka tattara sun nuna cewa matasa sun tsunduma harkar zumba kudi a caca, kuma abun ya zama musu jinin jiki
  • Wasu daga cikin waɗan na suka shiga caca, sun fara dana sani da kuma fatan daina wa nan gaba

Duba da yanayin tattalin arzikin da muke ciki, zuba kudi a harkar cacar wasanni a yanzu ya zama ruwan dare musamman ga mabiya manyan addinai biyu, Musulunci da Kiristanci.

Dailytrust ta tattaro cewa cacar wasanni a halin yanzun ya zama kasuwanci mafi sauki ga yan Najeriya.

Matasa da kuma manyan mutane daga kowane ɓangare sun jefa kansu cikin cacar wasanni yayin da kowane ke fatan zama zakara a ƙarshe.

Kowace caca, karshenta na zamo wa farin ciki ga wasu, yayin da wasu kuma ke shiga halin takaici da bakin ciki.

Buga caca
Yadda buga cacar wasanni ke mamaye zukatan yan Najeriya da cinye tattalin arzikinsu Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A shekaru da dama da suka wuce, masu buga caca suna zuwa shagunan da ake kira "Pool" da takardun shaida domin buga cacarsu.

Amma a halin yanzun, bisa samun cigaban fasaha ta kirkirar yanar gizo, kamfanonin caca sun samu cigaba da dama.

Adadi mai yawa na masu buga caca na da damar yin harkokinsu daga dakin kwanan su saboda cigaban da aka samu, wanda yasa kamfanonin caca suka ƙaru a Najeriya.

Kamfanonin caca a Najeriya

A ranar 7 ga watan Satumba, 2018, Hukumar kula da harkokin caca a Najeriya, (NLRC), ta bada lasisin gudanar da kasuwanci na farko ga kamfanin caca na AfriBet.

Zuwa yanzun akwai kamfanonin caca sama da 36 da suka samu lasisin kasuwanci a Najeriya.

Daga cikin irin waɗan nan kamfanonin akwai, Bet9ja, Betway, Nairabet, Naijabet, Betwinner, Betbigi, Cloud Bet, Sportybet, iBet, Access Bet, BetLion, Melbet, MerryBet, BetKing da ZeBet.

Waɗan nan kamfanoni na samun makudan kudi daga hannun yan Najeriya kuma sun faɗaɗa harkokin su zuwa kowane lungu da sako na kasar nan.

Da wahala a samu wani sashi na Najeriya da caca ba ta shiga ba, duk da rashin ingancin wutar lantarki, domin za'a iya buga caca a kan intanet da kuma a shaguna.

Duk da amfani da kamfanonin caca ke wa tattalin arzikin kasa, amma lamarin ya zama wata takobi mai kaifi biyu. Mutanen da caca ta zama musu jiki, asarar da suke yi ta zarce ribar da suka samu a tsawon shekarun da suka shafe.

Yadda caca ta shiga jinin mutane

A zahirin gaskiya, mutane da dama zasu ce caca ta zama jinin yan Najeriya, domin zai yi wahala mai buga caca ya iya faɗa maka lokacin da zai bari.

Wani mazaunin jihar Legas, Abbey, ya tsunduma cikin harkar cacar wasanni, yace yana zuba kudi a harkar caca akai-akai amma har yanzun bai taɓa amfana ba duk da mukadan kudin da yake zuba wa.

Yace:

"Na zuba kudi da yawa a caca, kuma ina samun nasara. Amma kudin da na samu ba su taka kara ba idan na kwatanta da waɗan da na kashe a ciki."
"A koda yaushe na samu kudi sai inji ina son buga wasan caca, akwai wanda ake buga wa da safe, akwai na dare da kuma na yamma. Na kan shiga da zaran na samu kudi."
"Haka lamrin ke zama da zaran ka fara sai ya zama jikin ka, zan iya cewa ta zama jikina idan ban yi ba bana jin daɗi."

Wani mai sana'ar haɗa takalmi, Seun Olaonipekun, wanda ya shiga harkar caca tun yana dalibi, ya tabbatar da cewa karshen kudin da ya taba zuba wa shine N25,000.

Yace:

"A wancan lokaci na kan yi amfani da kudin makaranta na na buga caca, ban taba samun nasara ba. Karshen kudin da na saka shine N25,000, kuma kuɗin makaranta na ne, ban san me yasa na yi haka ba."
Shagon caca
Yadda buga cacar wasanni ke mamaye zukatan yan Najeriya da cinye tattalin arzikinsu Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya abun yake a arewa?

Da yake zantawa da wakilin mu, wani mazaunin Kano, Sadiq Muhammad, yace wani abokinsa ne ya jefa shi a harkar caca.

Ya bayyana cewa manyan kudin da ya taba ci shine Naira N150,000 amma ya zuba kuɗaɗensa da suka kai N600,000.

Sadiq yace:

"Zan so in daina caca amma ta riga ta shiga jini na, duk da na yi asara da yawa, amma da zaran na sha gumi na, na samu kudi zanje in buga, saboda tana saka ni nishadi."

Bilal Abubakar, wanda yace ta hanyar zuba kuɗi a cacar wasanni ne ya fahimci a abinda ake nufi da nasara da faɗuwa a harkar caca, ya bayyana dana saninsa na fara harkar tun farko.

A cewarsa, son gudanar da rayuwar alfarma da wadaka da kuɗaɗe ne suka jefa shi cikin harkar caca, wanda a yanzun ya fara dana sani.

Yace:

"Duk wanda bai fara zuba kudi a caca ba, ina bashi shawarar kada ya kuskura ya fara. Caca wani wasa ne da zaka iya nasara ko ka faɗi, har yanzun ina dana sanin shiga caca."

Masu shagunan buga caca sun yi martani

Wani mai shagon buga caca, Shadrack Mark, yace yana fatan watarana ya cika burinsa a sana'ar caca, "Na san waɗan da suka ci makudan kudi, kuma ina fatan wataran nima zan samu, ba zan iya daina wa ba."

Hakanan kuma wani ɗan jihar Bauchi, Sadik Abubakar wanda malamin makaranta ne yace:

"Na fara caca a 2007 lokacin da abokina ya bani labari, na ɗauke ta a nishaɗi kuma sha'awar kwallom kafa ta jefa ni cikin harkar tsundum."
"Na samu nasara a lokuta da dama, amma yanzun ina kokarin daina ta ne kwata-kwata saboda addini na ya haramta caca."

Da yake nasa tsokacin, wani ɗalibin jami'ar ABU Zariya, Amar Isam'il, yace mafi yawan yan Najeriya sun ɗauki caca a matsayin hanyar gudanar da rayuwarsu saboda rashin aikin yi.

"A yanzun kamfanonin caca na kara mamaye Najeriya ne saboda makudan kudin da suke samu da wakilan su. Mafi yawan yan Najeriya ba su da aikin yi, dan haka sai sun buga caca suke samun kuɗi."

Wane shiri gwamnati ke yi kan caca?

Hukumar gwamnatin tarayya dake da alhakin kula da ayyukan caca a kasan nan, ta bayyana cewa tana gab da halatta caca a Najeriya.

A baya-bayannan hukumar NLRC ta yi gargaɗin cewa a daina jefa kananan yan Najeriya cikin harkar caca.

A sanarwan da ta fitar hukumar ta yi gargaɗin cewa:

"Matukar baka kai shekarun kaɗa kuri'a lokacin zaɓe ba, to shekarun ka ba su isa buga caca ba."

Duk wani yunkuri na jin ta bkin jami'in hulda da jama'a na hukumar, Mr Magnus Ekechukwu, bai samu nasara ba, domin jin yadda kamfanonin caca ke biyayya da dokoki.

A wani labarin na daban kuma An tsinci gawar wani mutumi mai aure, da wata Amarya a cikin mota a Kano

Rahotanni daga jihar Kano sun bayyana cewa an tsinci gawar wasu mutum biyu, mace da namiji a cikin mota.

Hukumar yan sanda tace namijin yana da mata har da ƴaƴa, yayin da ita kuma macen za'a ɗaura mata aure a watan Disamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel