Mutane sun huta da wahalar man fetur, Zeetin za su fara hada motocin da ke aiki da lantarki

Mutane sun huta da wahalar man fetur, Zeetin za su fara hada motocin da ke aiki da lantarki

  • Kamfanin Zeetin Engineering yace zai rika kera motoci masu amfani da wutar lantarki a garin Abuja
  • Wannan kamfani ya kashe kusan Naira biliyan 3.5 a Abuja, kuma ya na neman gudumuwar bankuna
  • Idan Zeetin Engineering sun dace, za su rika kera har da kayan karafuna na motoci da kuma jirage

FCT, Abuja - Wani kamfanin fasaha mai suna Zeetin Engineering, yana kafa wurin kera motoci a garin Idu da ke babban birnin tarayya Abuja.

The Cable tace Zeetin Engineering zai rika kera motoci masu amfani da wutar lantarki a Najeriya.

Wani babban jami’i na Zeetin Engineering, Robert Azibaola ya shaida cewa sun kashe sama da Naira biliyan 3.5 wajen gina wannan kamfani.

Da yake magana da manema labarai a ranar Alhamis, 25 ga watan Nuwamba, 2021, Robert Azibaola yace ba a ci bashi wajen wannan aiki ba.

Kara karanta wannan

Karyar takunkumi Gwamnati ke yi, Sanatoci sun gano ana daukar yaran manya aiki a boye

Sai dai Mista Azibaola yace zai yi sha’awar samun gudumuwa daga bankuna domin karasa wannan aiki da kamfanin Zeetin Engineering ya dauko.

Motocin da ke aiki da lantarki
Motoci masu aiki da lantarki Hoto: www.weforum.org
Asali: UGC

A cewar ma’aikacin kamfanin, bankunan gwamnati na BOI da NEXIM duk sun nuna sha’awar ba su aron Naira biliyan 2.5 domin aikinsu ya tafi.

"Manufa ta in ga cewa Najeriya ta cigaba."

“Idan ba mu dage ba, bakin mutum ba zai je ko ina a Duniya ba, duk da cigaban da ake samu a kasashen yammacin Duniya.”
“Ta haka ne zan bada gudumuwa ta wajen ganin Najeriya ta cigaba. A matsayin mai hangen nesa, wannan ce manufa ta, in ga an cigaba.” – Azibaola.”

Za a samu kamfanin OEM a Najeriya

Jaridar tace Zeetin ya kama hayar zama babban kamfanin OEM mai kera kayan motoci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Bankin Afrika zai ba Gwamna Ganduje Dala miliyan 110 domin ayi ayyuka a kauyukan Kano

Idan an gama wannan aiki, bayan motocin da za a rika fitowa da su, kamfanin zai rika kera bangarorin mota ta yadda ba sai an je kasashen waje ba.

A halin yanzu ana fama da karancin irin wadannan kamfani. Wannan ya sa ake fita waje domin sayen karafunan motoci, jirage, dogo da kayan gona.

Libya ta yi wa Najeriya kafa

Rahotanni sun bayyana cewa Libya ta sha gaban Najeriya wajen hako mai, sannan ta fara karbe mata kamfanonin wajen da suke aikin hako danye man.

Wasu manyan kamfanonin da suke kasuwanci a Neja-Delta sun tashi, sun koma yankin na Arewacin Afrika, inda za su bunkasa tattalin arzikin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel