Cire tallafin mai: NNPC zai samar da motocin bas saboda rage radadi ga 'yan Najeriya

Cire tallafin mai: NNPC zai samar da motocin bas saboda rage radadi ga 'yan Najeriya

  • Hanyoyin sufuri mafi sauki a Najeriya, tituna kenan suna isar da sama da kashi 80% na dukkan zirga-zirgar ababen hawa a kasar
  • Yayin da gwamnatin Najeriya ke yunkurin cire tallafin man fetur a watan Fabrairun 2022, ana fargabar tsadar sufuri zai biyo baya
  • Yanzu haka dai NNPC na kokarin shawo kan lamarin ta hanyar bai wa babban kamfanin kera motoci na Innoson kwangilar kera daruruwan motocin bas din da a za kai jihohi

Abuja - Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC), ya ba kamfanin Innoson Vehicle Motors (IVM) kwangilar kera wasu nau'ikan motocin bas na Gas (CNG) don magance illar cire tallafin mai a shekara mai zuwa.

Shugaban kungiyar Innoson, Cif Innocent Chukwuma ne ya bayyana hakan ga manema labarai kwanan nan a Nnewi, jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Mutane sun huta da wahalar man fetur, Zeetin za su fara hada motocin da ke aiki da lantarki

Cikin motocin da ake kera wa
Cire tallafin man fetur: Kamfanin NNPC zai tura daruruwan motocin bas na zirga-zirga a fadin kasar | Hoto: Innoson
Asali: Facebook

Yace:

“Ina kera wa NNPC motocin bas na birni. Wadanda za su yi amfani da iskar gas. Cikin rukuni 100. Ina kera su tun daga farko har karshe. Gas ne zalla.
"Amma ina yin su ne ta yadda idan aka samu karancin iskar gas za su iya amfani da dizal. Don haka, yana iya canzawa a matsayin zabi."
Injin CNG na sabbin motocin NNPC
Cire tallafin man fetur: Kamfanin NNPC zai tura daruruwan motocin bas na zirga-zirga a fadin kasar Hoto: Innoson
Asali: Facebook

Ya kara da cewa:

"Zan iya kera motoci masu amfani da wutar lantarki kuma in mai da iskar gas a madadin mai. Ina so in fara kera motoci masu amfani da wutar lantarki, amma har yanzu Najeriya ba ta shirya ba.
"Duk lokacin da Najeriya ta shirya, zan samar da su. Na yi nazari kuma na horar da mutane a kai. Wannan ci gaba ne mai kyau kuma a shirye muke mu yi shi”.

Kara karanta wannan

Kamfanonin Duniya sun tattara Dalolinsu, sun bar Najeriya zuwa wasu kasashen Afrika

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da shirin daukar nauyin sauya motoci miliyan daya zuwa aiki da iskar gas.

Babban jami’in NNPC, Mele Kyari, ya sanar a watan Disambar 2020 cewa ma’aikatar man fetur za ta samar da tsarin ayyukan canjin kyauta don baiwa motoci damar canjawa daga amfani da man fetur zuwa iskar gas.

Da yake magana da Arise TV kwanan nan kan batun, Chukwuma ya ce:

“Yanzu ina kera wasu motoci da injunan CNG na kamfanin NNPC. Na kusan kammala kera su kuma na yi su mafi kyawun motocin CNG kuma an gina su daga masana'anta ta.
“CNG za ta taimaka wa kowa saboda amfani CNG ya fi mai. Idan mutane za su iya canzawa zuwa CNG, zai amfani al'umma, farashin sufuri zai ragu. Najeriya na da dimbin CNG da ba ke zube birjik."

IVM tana da masana'anta a Nnewi, Kudu maso Gabashin Najeriya wanda ke iya samar da motoci 60,000.

Kara karanta wannan

Ba zamu taba yarda a kara farashin man fetur ba, Kungiyar Kwadago NLC

Farashin man fetur: Kasashen Afrika 10 da suka fi Najeriya tsadar man fetur

A wani labarin, a makon nan ne gwamnatin Najeriya ta bayyana yiyuwar cire tallafin man fetur a shekara mai zuwa, duba da yawan kudaden da gwamnatin ke kashewa wajen samar 'yan kasa mai.

Lamarin ya haifar da cece-kuce daga 'yan Najeriya, inda miliyoyin 'yan kasar suka bayyana rashin jin dadinsu ga wannan yunkuri.

Domin rage wa talakawa radadin cire tallafin, gwamnati tace za ta ware wasu kudade domin ba 'yan Najeriya alawus na zirga-zirga wanda ya Kai N5000 a duk wata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel