Miyagun ‘Yan bindiga sun sace ‘Yar shekara 3, sun bukaci a biya fansar Naira Miliyan 20

Miyagun ‘Yan bindiga sun sace ‘Yar shekara 3, sun bukaci a biya fansar Naira Miliyan 20

Wadanda suka yi garkuwa da wata yarinya a jihar Ondo mai suna Mary Fasina sun tuntube iyayenta

‘Yan bindigan sun bukaci a biya Naira miliyan 20 idan ana so wannan yarinya mai shekara 3 ta fito

Iyayen Mary Fasina sun roki masu garkuwa da mutanen su rage kudin fansar, amma hakan ya gagara

Ondo - Wadanda suka sace Mary Fasina, ‘yar karamar yarinya mai shekara uku a Duniya, sun bukaci a biya kudi kafin su fito da wannan yarinya.

Vanguard tace ‘yan bindigan da suka yi garkuwa da Mary Fasina sun nemi a biya su Naira miliyan 20.

Wata majiya ta shaidawa manema labarai cewa ‘yan bindigan da suka dauke Fasina sun tuntubi iyayenta, sun bukaci su tara masu Naira miliyan 20.

Hakan na zuwa ne sa’o’i kadan bayan an sace karamar yarinyar a gaban gidansu da ke garin Akure. Lamarin ya faru ne cikin dare a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga sun tayar da wani ƙauye bayan sun yi wa mutum 7 kisar gilla

Mahaifiyar yarinyar, Taiwo Fasina ta shaidawa Vanguard cewa yayin da aka zo bude mata kofar gida da ta dawo aiki, sai wasu suka yi gaba da ‘diyarta.

Gwamnan Ondo
Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu Hoto: BBCNewsHausa
Asali: Facebook

Mutanen da suka yi wannan aika-aika sun rufe fuskokinsu, suka bukaci mahaifiyar ta kwanta a kasa, daga nan suka dauke yarinyar suka yi tafiyarsu.

Kawo yanzu, ‘yan bindigan da ba a san su wanene ba, sun tabbatar da cewa Mary ta na hannunsu. Wani na kusa da iyayen yarinyar ya bayyana haka.

Yadda ta kaya da iyayen yarinya

“Sun tuntubi dangin na ta, sun yi waya da su, sun ce a ba su Naira miliyan 20, kafin su saki yarinyar ta je ga ‘yanuwanta.”
“Iyayen karamar yarinyar sun roki ‘yan bindigan su rage kudin da suka sa, amma sun nuna kunnen kashi, sun ki.” – Majiya.

Kara karanta wannan

Ku gaggauwa kawo miliyan N200m kafin mu bar wurin sabis, yan binidga sun gargaɗi iyalan dan sanda

‘Danuwan wannan yarinya da ta fada hannun miyagu yace tun daga wannan lokaci da aka yi magana, ba a sake jin muryar wadannan mutanen ba.

Sannan sun bukaci cewa ka da a sanar da jami’an tsaro da ‘Yan Amotekun game da lamarin, idan har iyayen su na da bukatar sake sa ido a kan ‘diyarsu.

'Yan bindiga sun yi barna a Zamfara

Rahotanni sun bayyana cewa jiya ‘yan bindiga su ka addabi mazauna kauyen 'Yan Buki da ke karkashin karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.

Lamarin ya auku ne a jiya ranar Alhamis inda su ka halaka mutane bakwai. Baya ga haka 'yan bindigan sun yi garkuwa da wasu mutane a kauyen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel