Ku gaggauwa kawo miliyan N200m kafin mu bar wurin sabis, yan binidga sun gargaɗi iyalan dan sanda

Ku gaggauwa kawo miliyan N200m kafin mu bar wurin sabis, yan binidga sun gargaɗi iyalan dan sanda

  • Yan bindigan da suka sace matafiya a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja sun nemi iyalan wani ɗan sanda su biya fansa
  • Rahoto ya bayyana cewa maharan sun nemi a tattara musu miliyan N200 cikin awanni 6 kafin su bar gurin sabis
  • Barayin sun yi fatali da tayin miliyan N2m da iyalan suka yi, kuma sun gargaɗe su zasu iya harbe shi

Kaduna - Yan bindiga sun shaida wa iyalan ɗan sandan da suka sace su tattara musu miliyan N200m domin a sako shi saboda zasu bar wurin sabis.

Premium Times tace Dan sandan mai suna Dambo Hosea, na ɗaya daga cikin matafiyan da aka sace ranar Lahadi, a kan hanyar Kaduna-Abuja.

Shine jami'in dan sandan dake tare da tsohon ɗan takarar gwamnan Zamfara, wanda ƴan bindiga suka kashe yayin harin.

Kara karanta wannan

Wahalhalu 5 da 'yan Najeriya za su shiga idan man fetur ya koma N340, Shehu Sani

Yan bindiga
Ku gaggauwa kawo miliyan N200m kafin mu bar wurin sabis, yan binidga sun gargaɗi iyalan dan sanda Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Tsagerun yan bindigan sun nemi iyalai su tattara musu zunzurutun kudi miliyan N200m domin sako shi cikin gaggawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kiran da suka wa iyalan ɗan sandan ta wayar salula, ya bindigan sun bayyana cewa zasu bar wurin da ake samun sabis, dan haka a biya fansa cikin lokaci.

Yan bindigan sun yi fushi

Yayin da iyalan mutumin suka roki zasu biya miliyan N2m, maharan sun fusata kuma suka ba su awanni 6 kacal su kawo miliyan N200m.

Wakilin mu ya saurari yadda ta kaya a hirar iyalan ɗan sandan da kuma masu garkuwan. Lokacin da aka roki za'a basu N2m, sai suka ce:

"Bai kamata kuce haka ba bayan mun sace babban mutun kamar wannan, kuna faɗin abinda ba zai yuwu bane. Kun ci sa'a abokan aiki na ba su ji ba."
"Lamarin zai girmama idan kuka ƙi biyan bukatar mu, idan kuka sake faɗin miliyan biyu, to ko dai mu harbe shi ko kuma mu dake shi."

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun sake kai hari Filato, sun kashe mutane biyu

Dan sandan na cikin yanayi

Yayin da suka bashi damar yin magana, Hosea ya roki iyalansa su taimaka su biya kudin akan kari domin inda suke ba shi da kyau.

"Mun yi doguwar tafiya kafin mu samu sabis mu kira ku, kuje wurin abokanaina idan ba zaku iya haɗa kudin ba, ku ci bashi idan na dawo zan biya."

Da aka nemi wayar salulan kakakin yan sandan jihar Kaduna, Muhammed Jalige, ba'a same shi ba bare a ji ta bakin hukumar yan sanda.

A wani labarin kuma Sojoji sun hallaka yan ta'adda 90, sun damke kasurgumi da suke nema ruwa a jallo

Hedkwatar tsaro ta bayyana nasarorin da dakarun soji suka samu a yankin arewa maso gabashin Najeriya cikin mako biyu.

Daraktan watsa labarai na HQ, Bernard Onyeuko, yace sojojin sun hallaka aƙalla yan ta'adda 90, sun kame wasu 21.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262