Bauchi: Wani mutum ya halaka almajiri mai shekaru 11, ya cire kwakwalwarsa

Bauchi: Wani mutum ya halaka almajiri mai shekaru 11, ya cire kwakwalwarsa

  • Wani mutum wanda ba a san ko waye ba ya yi amfani da dutse wurin fasa kan almajiri tare da cire kwakwalwarsa
  • Mutumin ya ja almajiran biyu wani kebantaccen wuri ne inda ya buga wa daya dutse kafin dayan ya kubuce ya tsere
  • Ya sanar da mazauna yankin inda suka gaggauta zuwa wurin amma sai gawar almajirin mai shekaru 11 a kwance cikin jini

Bauchi - Wani mutum ya yi amfani da dutse wurin fashe kan wani almajiri mai shekaru 11 tare da cire kwakwalwarsa a yankin Kofar Wambai da ke kwaryar birnin Bauchi.

Daily Trust ta tattaro cewa, mazauna yankin sun ce wani bako ya kira wasu daliabai biyu tare da jan su zuwa wani kebantaccen wuri inda ya aikata aika-aikar.

Bauchi: Wani mutum ya halaka almajiri mai shekaru 11, ya cire kwakwalwarsa
Bauchi: Wani mutum ya halaka almajiri mai shekaru 11, ya cire kwakwalwarsa. Hoto daga dailytrust.com
Source: UGC

Daya daga cikin almajiran wanda ya sha da kyar, ya sanar da mazauna yankin abinda ya faru kuma sun hanzarta zuwa wurin amma sai suka tarar da gawar almajirin inda daga bisani suka sanar da 'yan sanda.

Read also

Da Duminsa: Masu garkuwa sun kashe tsohon mai neman takarar gwamnan Zamfara a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Mai Magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Bauchi, SP Muhammad Ahmad Wakil, ya ce "'Yan sanda sun samu kiran gaggawa daga wani mutumin kirki cewa wani mutum ya yi amfani da dutse inda ya fashe kan almajiri.
"Mutumin ne ya yaudari almajiran biyu, Muhammad Yunusa mai shekaru 11 da Aminu Yusuf mai shekaru 12 inda ya yi amfani da dutse tare da fasa kwakwalwar Yunusa."

Ya tabbatar da cewa 'yan sanda suna kokarin ganin sun cafke mutumin tare da bi wa yaron hakkinsa, Daily Trust ta ruwaito.

Innalillahi: An tsinta gawar limamin Abuja kusa da gona

A wani labari na daban, a ranar Alhamis hankula sun matukar tashi bayan an tsinta gawar limamin makabartar Kubwa mai suna Malam Abdurrashid Usman a gona inda ya je samo wa iyalinsa itace. Wani dan uwan mamacin mai suna Adamu Sama'ila, ya ce limamin ya bar gida wurin karfe goma na safe amma bai dawo ba, Daily Trust ruwaito hakan.

Read also

Innalillahi: An tsinta gawar limamin Abuja kusa da gona

Ya ce, "Matarsa ta fita domin ba ta gida a lokacin. Ta fita saide-saide. Ta gane cewa ba ya nan ne wurin karfe shida lokacin da ta dawo ba ta tarar da shi ba. Hakan yasa ta yi magana.
"Mun shiga daji wurin gonar Gado-Nasko daga karfe takwas har zuwa 12 na dare amma ba mu gan shi ba. Mun dai samu kayanshi, amalanken da yayi amfani da ita, gatarinsa da itace."

Source: Legit.ng

Online view pixel