Babbar Magana: Gwamnatin Buhari ta shirya sayarwa 'yan Najeriya gida mai daki daya N9m

Babbar Magana: Gwamnatin Buhari ta shirya sayarwa 'yan Najeriya gida mai daki daya N9m

  • Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin sayar da gidaje ga 'yan kasa na NHP tare da kirkirar da kafar yanar gizon sayar da gidajen da aka kammala
  • A cewar ministan gidaje, kafar shirin wacce ta kunshi bayanan gidaje masu daki daya, biyu da uku an tsara sayar dasu akan wani farashi
  • A halin da ake ciki, bincike ya nuna cewa gida mai daki daya yana kan farashin N9,268,751. Farashin iri daya ne a kowace jiha

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya bayyana farashin gidaje a shirin sayar da gidaje ga 'yan kasa wanda ya kunshi gidaje masu dakuna daya da biyu da uku.

A cewar ministan, gidajen da aka fitar sun hada da mai daki 1 mai fadin murabba’in mita 60, da daki 2 mai fadin murabba’in mita 76 da kuma mai daki 3 mai fadin murabba’in mita 110, inda ya kara da cewa sun fi abin da akasarin dillalai ke bayarwa, inji rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Aljannar duniya: Hotunan cikin katafarun gidajen £45m na Ronaldo da motocin alfarma

Babbar Magana: Gwamnatin Buhari ta shirya sayarwa 'yan Najeriya gida mai daki daya N9m
Tsarin ginin gwamnatin tarayya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Yace:

“Akwai mai dakuna 1, 2, 3, wasu daga cikinsu babba ne, yayin da wasu kuma a hade suke kanana. Mafi qarancin gida shine N7.2m mafi girma kuma shine kusan N16m."

Sai dai, rahoton bincike na TheCable ya nuna cewa gida mai daki daya yana kan farashin N9,268,751. Farashin iri duk daya ne a duk fadin jihohin da akwai nau'in ginin.

Gida mai daki biyu ana sayar da shi kan N12,398,460, yayinda mai daki uku ya kai 16,491,155.

Gida karami mai daki daya da ake da nau'insa a jihohin Kudu ana sayar da shi N7,222,404, mai daki biyu N9,148,378, yayin da mai daki uku ya kai N13,241,074.

Shirin sayar da gidaje

A baya kunji cewa, a ranar Jumu'a da ta gabata, 12 ga watan Nuwamba, gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin siyar da gidajen da ta gina ga yan Najeriya a farashi mai rahusa.

Kara karanta wannan

2022: Kano ta ware miliyan N800 domin magance talauci da rashin aiki a tsakanin mata

A cewar ministan, an kirkiri shafin ne domin tabbatar da yan Najeriya dake muradin mallakar gida, sun samu damar shiga tsarin.

A halin yanzun, kimanin gidaje 5,000 aka kammala kuma za'a siyar da su a rukuni na 1 da na 2 a jihohi 34 da Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel