Hukumar NECO ta rike jarabawan dalibai sama da 80,000 a jihar Kano, Ta fadi dalili

Hukumar NECO ta rike jarabawan dalibai sama da 80,000 a jihar Kano, Ta fadi dalili

  • Hukumar NECO ta rike jarabawar daliban jihar Kano sama da 80,000 saboda rashin biyan bashi na gwamnatin jihar
  • Rahotanni sun bayyana cewa sama da kashi 70 cikin dari na daliban iyayensu ke ɗaukar nauyinsu, amma bashin gwamnati ya rutsa da su
  • Wani dalibi da lamarin ya shafa yace sakamakon kaɗai yake jira don cigaba da bin matakan samun gurbin karatu a jami'a

Kano - Hukumar shirya jarabawan kammala sakandire ta ƙasa (NECO) ta rike sakamakon jarabawan dalibai sama da 80,000 yan asalin jihar Kano.

Vanguard tace NECO ta ɗauki wannan matakin saboda bashin da yake bin gwamnatin jihar da suka kai Naira Miliyan N500m.

Rahotanni sun bayyana cewa sama da kashi 70 cikin dari na ɗaliban da suka zauna jarabawar NECO 2021 iyayen su ne suka ɗauki nauyin biyan kudin.

Read also

Babu unguwar da babu yan kwaya a Najeriya, Janar Buba Marwa

Hukumar NECO
Hukumar NECO ta rike jarabawan dalibai sama da 80,000 a jihar Kano, Ta fadi dalili Hoto: channelstv.com
Source: UGC

Sai dai rashin biyan bashin miliyan N500m da gwamnatin jihar ta yi, ya jawo har yanzun sakamakon jarabawan su bai fita ba.

Jihar Kano na cikin jerin jihohin Adamawa, Neja da Zamfara, waɗan da suka rike wa NECO kuɗin jarabawa.

Ya daliban suka ji da wannan matsala?

Daya daga cikin ɗaliban da lamarin ya shafa, ya shaida wa BBC Hausa cewa:

"Muna cikin babban matsala saboda makarantun gaba da sakandire na gab da kammala bayar da gurbin karatu na wannan shekaran."
"Ina jiran sakamakon NECO ne domin cigaba da cike matakan samun gurbin karatu a jami'ar da nake so, amma zan iya rasa damar idan ba'a shawo kan matsalan ba."
"Mun yi kokarin tuntubar makarantar mu, amma sun faɗa mana mu cigaba da hakuri kuma lokaci kara kurewa yake. Ban san mai zai faru a gaba ba."

Read also

Babbar Magana: Tsagerun yan bindiga sun hallaka jami'an tsaro sama da 100 a jihar Benuwai

Duk wani kokarin na jin ta bakin kwamishinan ilimi na jihar Kano, Sanusi Saidu Kiru, ya ci tura, domin jin ta ɓangaren gwamnatin Kano.

A wani labarin na daban kuma Wani Dalibin jami'a ya lakadawa malamarsa duka kawo wuka daga neman taimako

Wani ɗalibi dake karantar kwas ɗin Microbiology a jami'ar Ilorin, (UniLorin) ya lakaɗawa lakcaransa mace dukan kawo wuka.

Dailytrust tace Ɗalibin mai suna, Captain Walz, bai samu damar yin kwas ɗin neman sanin makamar aiki ba (SIWES), dan haka yaje neman taimakon lakcaran.

Source: Legit.ng

Online view pixel