Ya kwace mana matanmu na aure, Mazaje sun kai karar wani Fasto

Ya kwace mana matanmu na aure, Mazaje sun kai karar wani Fasto

  • Tashar Human Right Radio ta wallafa yadda mutane suke zargin Fasto Harrison Anazodo Charles da kwace musu matansu
  • Hoto ya bayyana mazajen wasu mata da suka kai sa kara tashar rediyon inda suka bayyana abinda ya faru da matansu
  • Daya daga cikinsu ya bayyana cewa haka kawai matarsa ta fara kwashe kayanta inda tace Fasto ne ya bata umurnin haka

Tashar Human Right Radio wacce aka fi sani da Brekete Family dake Abuja ta daura hotunan wasu mazaje da suka kai karar wani Fasto Harrison Anazodo Charles kan laifin kwace musu mata, da 'yayansu.

A cewar Brekete Family, mazajen sun zargi Faston da sihirce musu mata.

Daya daga cikinsu yace:

"Iyalina ta dawo daga Coci ta sanar da ni cewa Fasto ya fada mata daga yanzu aurenta da mijinta ya mutu."

Kara karanta wannan

Ba haka aka haifeni ba, Samari ko sha'awa ta ba sa yi: Budurwa ta bayyana

Ta fita daga gidan

Ya kara da cewa lokacin da ta fada masa haka, ya dauka wasa take yi. Amma daga baya ta kwashe kayanta gaba daya daga gidan.

Ya kwace mana matanmu na aure
Ya kwace mana matanmu na aure, Mazaje sun kai karar wani Fasto Hoto: @tattleroomng
Asali: Instagram

Nima ya kwashe min mata da dukkan 'ya'yana

Wani mutumi daban ya bayyana cewa shima haka ya faru da shi kimanin shekaru goma da suka gabata lokacin da matarsa ta ce aurensu yazo karshe.

Mijinta yace matarsa ta kwashe yara ta tafi da su gidan Fasto Harrison Anazodo Charles.

Duk yunkurin da yayi na magance matsalar ta hanyar kai kara wajen yan sanda ya ci tura. Kai a karshe ma shi yan sanda suka daure.

Yan Najeriya sun tofa albarkatun bakinsu

Adamsy Jibril EL-sese Biu:

"Uhmmm, fasto na gaskiya baya aikata hakan saidai Daman a ko ina Kuma a kowani irin addini ana samun na banza da nagari, Amma wannan fasto yanaso ya batawa wasu fasto suna ne kawai gaskiya sbd duk inda akace maka wannan shugaba ne toh wasu Sai a hankali suna amfani da matsayin su saisu cutar da wasu

Kara karanta wannan

Bidiyon ango da ya fashe da kuka yayin da yake taka rawa tare da mahaifiyarsa a wajen bikinsa

Allah yasa mufi karfin zuciyar mu Kuma Allah yasa mu mutu cikin musulunci Ameeeen thumma Ameeeen"

Maryam Abubakar tace:

"Gaskiya Bai kyauta ba, saboda malamin addini ne shi yasa suka bashi Amana amma Yaci Amana.sune masu batawa sauran suna."

Saminu Nuhu yace:

Idan 6era dasata daddawa nada wari, kuma dalaifinku meyasa kukabar matanku suna rawa suna girgiza agaban fasto, shikuma faston nan badutse bane dole yagani ya yaba, dagaqarshe yaza6a yadarje yacigaba dashan shagalinsa, yabarku agefe kunazare ido kamar anyiwa kuturu gorin zuwa makka

Sidi Muhammad yace:

Yakamata masu bada tarbiyya ta kowanne irin addini surin abinda mabiyansu zasu gamsu da halayyarsu.cikin aminci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel