Labari da duminsa: Hotunan mummunan fashewar butalin iskar gas a Legas, ana fargabar wasu sun mutu

Labari da duminsa: Hotunan mummunan fashewar butalin iskar gas a Legas, ana fargabar wasu sun mutu

  • Wasu 'yan Nigeria sun rasa rayyukansu a jihar Legas bayan fashewar butulin iskar gas da ya faru a unguwarsu
  • A cewar rahotanni, lamarin ya faru ne a Ojekunle Streer, Papa Ajao misalin karfe 8 na safiyar ranar Talata
  • Kazalika, rahotanni sun yi ikirarin cewa akwai yiwuwar wasu mutanen suna can sun makale daga wurin da abin ya faru

Jihar Legas - Ana fargabar mutane da dama sun mutu sakamakon fashewar butalin iskar gas da ya faru a Ojekunle Street, Papa Ajao Legas a safiyar ranar Talata.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa fashewar gas din ya faru ne misalin karfe 8 na safiyar ranar Talata.

Labari da duminsa: Fashewar butalin iskar gas ta jawo tashin hankali a Legas, ana fargabar wasu sun mutu
Fashewar butalin iskar gas ta jawo tashin hankali a Legas, ana fargabar wasu sun mutu. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Hakazalika, rahotonni sun kara da cewa an fitar da mutane da dama daga wurin da abin ya faru ana kuma fargabar har yanzu akwai wadanda suka makalle.

Kara karanta wannan

Manyan gobe: Hazikan matasa 'yan Najeriya 3 da suka kera motocin a zo a gani da kansu

Labari da duminsa: Fashewar butalin iskar gas ta jawo tashin hankali a Legas, ana fargabar wasu sun mutu
Hotunan mutane a wurin da butalin gas ya fashe a Legas. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Labari da duminsa: Fashewar butalin iskar gas ta jawo tashin hankali a Legas, ana fargabar wasu sun mutu
Fashewar butalin gas a Legas ya tada hankula. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Labari da duminsa: Fashewar butalin iskar gas ta jawo tashin hankali a Legas, ana fargabar wasu sun mutu
Yadda mutane suka yi cincirindo bayan fashewar butalin gas a Legas. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

A wani rahoton, wani da ya tsira yayin fashewar bututun iskar gas a Legas ya bayyana ukubar da ya sha sakamakon mummunan abin da ya faru a daren ranar Alhamis.

Mutumin wanda ya ce sunansa Peter ya bayyana yadda ya sha da kyar a lokacin da ya ke kusa da motarsa a OPIC Plaza kwatsam ya ji kafarsa ta yi sanya.

A hirar da ya yi da The Punch a ranar Juma'a 18 ga watan Yuni, ya yi ikirarin cewa a lokacin da ya fito daga motarsa misalin karfe 11 na dare, ya hangi babban motar dauke da gas a gaban OPIC Plaza.

Ya cigaba da cewa tsoro ya kama shi bayan ganin yadda gas din ya bade dukkan wurin.

Ku dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel