Yanzu-Yanzu: ASUU ta yi barazanar zuwa sabon yajin aiki, ta bawa gwamnati wa'adin sati 3

Yanzu-Yanzu: ASUU ta yi barazanar zuwa sabon yajin aiki, ta bawa gwamnati wa'adin sati 3

  • Kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU ta ba gwamnatin tarayya makwanni 3 don cike mata sharuddanta wadanda su ka sa hannu tun watan Disamban 2020
  • ASUU ta ce matsawar gwamnatin bata biya wa kungiyar bukatunta ba, za ta dauki tsattsauran mataki sakamakon rashin cika mata alkawura da gwamnatin ta yi
  • Har ila yau, kungiyar ta kirkiri wani kwamitin bincike akan matsayin da jami’ar kimiyya da ke Owerri ta bai wa ministan sadarwa, Dr. Isa Ibrahim Pantami

Kungiyar malaman jami’o’i na Najeriya ta ASUU ta bai wa gwamnatin tarayya makwanni 3 don cika mata sharuddan da ta gindaya wa gwamnatin, The Nation ta ruwaito.

Ta bayyana wannan kudirin nata ne inda ta ce wajibi ne gwamnatin ta cika mata alkawarran da su ka sa hannu akai tun ranar 23 ga watan Disamban 2020.

Kara karanta wannan

Jinsi ba shamaki bane: Injiniya mace 1 cikin maza ta sanar da gwargwamayar da ta sha duk da maraicinta

ASUU ta ce in har gwamnatin bata cika sharuddan na ta ba cikin makwanni 3 za ta dauki tsattsauran mataki.

Har ila yau kungiyar ta kafa kwamiti mai zaman kansa don bincike akan matsayin da aka bai wa ministan sadarwa.

Yanzu-Yanzu: ASUU ta yi barazanar zuwa sabon yajin aiki, ta bawa gwamnati wa'adin sati 3
ASUU ta yi barazanar zuwa sabon yajin aiki, ta bawa gwamnati wa'adin sati 3. Hoto: Festus Keyamo
Asali: Facebook

Dama jami’ar tarayya ta kimiyya da ke Owerri ta kara wa ministan matsayi zuwa farfesa a bangaren tsaron yanar gizo.

Rashin gamsuwa da matsayin yasa kungiyar ASUU din ta kafa kwamiti don bincike akan cancantar ministan.

A wani rahoton da The Guardian ta wallafa, Farfesa Emmanuel Osodeke, shugaban ASUU ya bada sanarwar ne bayan taron kungiyar ta NEC da aka yi a jami'ar Abua a ranar Asabar 13 ga watan Nuwamba da Lahadi 14 ga watan Nuwamba.

Osodeke, ya koka kan cewa duk da taron da suka yi da ministan kwadago da ayyuka, Dr Chris Ngige har yanzu manyan bukatun da suka so a biya musu sunan nan ba a ce komai ba.

Kara karanta wannan

Jaruma Rahama MK, matar gwamna a fim din Kwana Casa'in ta yi auren sirri

Akwai yiwuwar a shiga sabon yajin aiki a yayin da ASUU ke zargin FG da rashin cika alkawari

Hakan na zuwa ne bayan ASUU, a ranar Talata, 21 ga watan Satumba ta ce gwamnatin tarayyar ba ta tanka mata bisa gargadin da ta bada a watan Yuli.

Emmanuel Oshodoke, shugaban ASUU na asa ya ce gwamnatin tarayyar bata aiwata da yarjejeniyar da suka cimma ba.

Kungiyar, a ranar Asabar, 19 ga watan Yuli ta bawa FG sabon wa'adi, na cewa ta biya dukkan albashi da allawus na mambobinta idan ba haka ba ta shiga yajin aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel