Yadda Bankuna 2 suka taimakawa Abdulrasheed Maina ya sacewa ‘Yan fasho Naira Biliyan 2

Yadda Bankuna 2 suka taimakawa Abdulrasheed Maina ya sacewa ‘Yan fasho Naira Biliyan 2

  • A farkon makon nan aka samu Abdulrasheed Maina da laifin satar dukiyar ‘yan fansho a Najeriya.
  • Okon Abang yace Abdulrasheed Maina ya saci wadannan kudi ne da taimakon wasu bankuna biyu.
  • Bankunan da Maina ya bude akawun sun ga biliyoyi su na yawo, amma ba su sanar da hukuma ba.

Abuja - Abdulrasheed Maina, jami’in da ya shugabanci kwamitin gyaran fansho a Najeriya zai yi zaman kaso bayan kama shi da laifin satar Naira biliyan biyu.

Wani rahoto da Yahoo da Quartz Africa suka fitar a ranar Laraba, 10 ga watan Nuwamba, 2021, ya nuna cewa bankuna sun bada gudumuwa wajen satar kudin.

Da yake zartar da hukunci a ranar Litinin, Alkalin babban kotun tarayya na Abuja, Okon Abang, ya yi tir da sakacin bankunan da aka yi amfani da su wajen barnar.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar Gwamnati ta sasanta da Nnamdi Kanu da Igboho a wajen kotu – Malami

Okon Abang yace Abdulrasheed Maina ya wawuri Naira miliyan 300, Naira miliyan 500 da kuma Naira biliyan 1.5 duk ta asusun da ya bude a wasu bankuna biyu.

Legit.ng Hausa ba za ta iya kama sunan wadannan bankuna ba, sai dai suna cikin bankunan da suka fi shahara a Najeriya, dayan ma ya yi suna a nahiyar Afrika.

Abdulrasheed Maina
Abdulrasheed Maina Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

‘Yanuwan Abdulrasheed Maina ne amintattun wadannan asusu da ya bude, sai sun sa hannu sannan kudi zai iya fita, amma bankunan ba su dauki mataki ba.

Meya hana bankunan su rasa lasisinsu?

A ka’ida ya kamata ace bankunan sun shigar da kara da suka ga kudi masu yawa sun shigo. Wannan sakaci yana iya jawo a karbe masu lasisin aiki a Najeriya.

Majiyarmu tace abin da ya ceci bankunan shi ne EFCC ba ta hada da su a karar da ta shigar ba.

Kara karanta wannan

Masu garkuwa da mutane sun kashe wani kyaftin din soji mai ritaya

Dokar hana safarar kudi ta shekarar 2011 tana kokarin magance irin wadannan aika-aika. Kuma an shigo da tsarin BVN domin a hana mutane bude akawun a boye.

Bankunan sun taimakawa Maina wajen yawo da wadannan makudan kudi duk da cewa sun san adadin kudin ya zarce albashin ma’aikaci irinsa (N300, 000 a wata).

SARS ta kashe wani matashi a Kotu

A jiya aka zo karshen shari’ar da ake yi tsakanin Abba Hikima esq. da ‘yan sanda kan kisan wani matashi da ake zargin dakarun SARS sun yi tun a shekarar 2019.

Lauyan mai kare hakkin Bil Adama yace ya yi nasara a kan ‘Yan Sandan jihar Kano a gaban kotu, bayan Alkali yace a biya 'yanuwan wanda aka kashe diyyar N50m.

Asali: Legit.ng

Online view pixel