Da Dumi-Dumi: Kotu ta dage shari'ar Nnamdi Kanu zuwa shekara mai zuwa 2022

Da Dumi-Dumi: Kotu ta dage shari'ar Nnamdi Kanu zuwa shekara mai zuwa 2022

  • Babbar kotun tarayya ta sanar da ɗage zaman sauraron shari'ar shugaban IPOB, Nnamdi Kanu har zuwa shekara mai zuwa
  • Mai shari'a Binta Nyako dake jagorantar shari'ar, ita ce ta sanar da haka a zaman yau wanda bai ɗauki tsawon lokaci ba
  • Sai dai Kanu ya shaida wa kotun cewa har yanzun jami'an tsaron farin kaya DSS sun hana lauyansa daga Amurka ya ganshi

Abuja - Babbar kotun tarayya dake zamanta a birnin tarayya Abuja ta ɗage zaman sauraron shari'ar shugaban ƙungiyar yan aware, IPOB, Nnamdi Kanu, zuwa sabuwar shekara.

BBC Hausa ta rahoto cewa mai shari'a Binta Nyako, ta ɗage sauraron karar zuwa ranakun 19 da 20 ga watan Janairu, 2022.

Gwamanatin tarayya ce ta shigar da ƙarar shugaban yan awaren, bisa zarginsa da aikata manyan laifuka da suka haɗa da tada kayar baya da ta'addanci.

Read also

Da dumi-dumi: Jami’an tsaro sun hana lauyan Kanu, yan jarida da shugabannin Ibo shiga harabar kotu

Kanu a Kotu
Da Dumi-Dumi: Kotu ta dage shari'ar Nnamdi Kanu zuwa shekara mai zuwa 2022 Hoto: @Ndi Igbo
Source: Facebook

Yadda zaman kotun ya gudana

Rahotanni sun bayyana cewa Lauyoyin Kanu sun ɗauki zafi, inda suka fice daga harabar kotun tun kafin mai shari'a ta ƙaraso.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban IPOƁ, Nnamdi Kanu, ya shaida wa kotun cewa jami'an hukumar DSS sun kekashe ƙasa sun hana lauyansa daga ƙasar Amurka shiga zaman kotun.

Sai dai a nata ɓangaren, Mai shari'a Binta Nyako, ba ta ɗauki wani lokaci mai tsawo ba, ta sanar da ɗage sauraron ƙarar zuwa watan farko na shekarar 2022.

Sau 5 kenan ana hana ni shiga - Lauya

Lauyan Kanu, da ya zo daga ƙasar Amurka, yace hana shi shiga kotu da jami'ai suka yi yau shine karo na biyar tun bayan zuwansa.

A cewar Bruce Fein, shi kaɗai jami'an suka ware suke hana shi shiga zaman kotun, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Read also

Zaben Anambra 2021: Akwai sauran rina a kaba, inji dan takarar PDP, Valentine

A jawabinsa yace:

"Ni ne lauyansa daga Amurka, karo na biyar kenan ana hana ni ganin Kanu duk kuwa da cewa ana barin dukkanin lauyoyinsa su gan shi."

Tawagar lauyoyin Kanu, sun yi barazanar canza kotu, domin a ganinsu wannan kotun ba zata wa wanda suke kare wa adalci ba.

A wani labarin kuma Dakarun Sojoji sun bude wa mayakan ISWAP wuta a kan hanyar Maiduguri

Rahotanni sun bayyana cewa an yi dogon musayar wuta tsakanin mayakan Boko Haram/ISWAP da Sojoji a Maiduguri.

Wani direba ya bayyana cewa dole tasa suka yi cikin daji da motocin su yayin da suka jiyo ƙarar harbe-harbe.

Source: Legit.ng

Online view pixel