Watanni da sauke Ibrahim Magu daga kujerar EFCC, ya na karbar albashi a kowane wata

Watanni da sauke Ibrahim Magu daga kujerar EFCC, ya na karbar albashi a kowane wata

  • Rahotanni sun ce har gobe ana cigaba da biyan Ibrahim Magu kaso daga cikin albashinsa a duk wata
  • Watanni 16 da suka wuce ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Magu daga aiki
  • A ka’idar aikin gwamnati, ana biyan jami’in da aka dakatar rabin albashin, har sai an gama bincike.

FCT, Abuja - Watanni goma sha shida da dakatar da Ibrahim Magu daga matsayin shugaban EFCC, Jaridar Punch tace har yanzu ana biyan shi albashi.

Rahoton ya bayyana cewa Ibrahim Magu yana karbar rabin albashinsa duk wata, duk da ya bar kujerar mukaddashin shugaban hukumar ta EFCC.

A ka’idar aiki, ana biyan ma’aikaci 50% na albashinsa ne a duk lokacin da ake bincikensa da wani laifi, har sai lokacin da aka kammala binciken na sa.

Read also

An kaure tsakanin jami'an EFCC da na gidan yari kan wa zai tafi da Maina magarkama

A dokar aikin gwamnati, sakataren din-din-din zai iya sa a rika biyan ma’aikaci rabin albashinsa idan ya aikata laifin da zai iya kai ga korarsa daga aiki.

Ibrahim Magu
Ibrahim Magu a wajen wani taro Hoto: pmnewsnigeria.com
Source: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abin da dokar gwamnatin tarayya ta ce

“Idan aka samu ana zargin jami’i da babban laifi da zai iya kai ga kora daga aiki, sakataren din-din-din zai iya dakatar da shi daga ofis.”
“Sai ya sa a rika biyan shi rabin albashinsa na wata, har tsawon lokacin da aka kammala binciken na sa, ko a dawo da shi bakin aiki.”

A watan Yulin 2020 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da dakadar da Ibrahim Magu saboda zargin rashin kunya da rashin gaskiya.

Ministan shari’a, Abubakar Malami, SAN ne ya jefi shugaban na EFCC a lokacin da zargi. Daga baya shugaban kasa ya nada kwamiti ya yi bincike.

Read also

Kotu ta daure lauya shekaru 15 bisa laifukan tafka karya a gaban kotu

Gwamnati ba ta dauki mataki kan rahoton da aka gabatar ba. Wannan ya jawo aka ki yi wa Magu karin matsayi zuwa matakin AIG a aikin ‘dan sanda.

Kwamitin Ayo Salami ne ya binciki Ibrahim Magu, da ya kammala aikinsa, sai ya gabatar da rahoto.

Me Ibrahim Magu yake fada bayan cire shi?

Kwanakin baya an ji lauyan tsohon shugaban riko na hukumar ta EFCC, Tosin Ojaomo, yana cewa ba a yi adalci ba wajen yadda aka dakatar da Magu ba.

Ojaomo ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin 'Politics Today'. Lauyan ya koka a kan yadda aka ki bayyana sakamakon binciken.

Source: Legit.ng

Online view pixel