Yanzu Yanzu: Magu ya yi jawabin farko bayan sakinsa

Yanzu Yanzu: Magu ya yi jawabin farko bayan sakinsa

Dakataccen mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Ibrahim Magu, ya yi magana a kan radadin da ya ji yayinda aka tsare shi.

Magu ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su yanke kauna da yaki da rashawa.

Ya ce imma yana a matsayin shugaban EFCC ko akasin haka, “ya zama dole ‘yan Najeriya su rungumi yaki da rashawa, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajirce domin kawar da shi.”

Tsohon shugaban na EFCC ya ce abun da ya fuskanta na “daya daga cikin hadarurrukan da ke tattare da aikin.”

Ya ce dukkanin zarge-zargen da ke yawo duk don a bata sunansa da na EFCC ne.

Yanzu Yanzu: Magu ya yi jawabin farko bayan sakinsa
Yanzu Yanzu: Magu ya yi jawabin farko bayan sakinsa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Magu, wanda ya yi magana a wata hira ta musamman da jaridar The Nation ya ce: “Ta bangarena, zan yi yaki da rashawa har abada. Ina kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da goyon bayan yaki da rashawa.

“Kada su karaya a yakin saboda rashawa na kashe kasa fiye da dukkanin wani abu.

“Ba yakin son zuciya bane. Imma Ina a matsayin shugaban EFCC ko akasin haka, dole a ci gaba da yakar rashawa.

“Abunda na fuskanta ya kasance lamari na "kura ta ci kura" amma Ina kallonsa a matsayin daya daga cikin hadarurrukan da ke tattare da aiki. Amma kada mu karaya."

KU KARANTA KUMA: Nan bada dadewa ba za a rasa ma su karfin gwuiwar yaki da cin hanci - Osinbajo

Kan zargin da ake masa, ya ce: “Duk zancen banza ne. Tarin zarge-zarge ne kawai domin bata mani suna da EFCC. Ban saci kudi ko karkatar da kudi don amfanin kaina ba. Na karanta zarge-zargen kuma na shiga juyayi.

“Ina godiya ga ‘yan Najeriya a kan goyon bayansu, kada su karaya. Ina farin ciki da dawowa, na yi imani za a yi nasara a yaki da rashawa.”

A yau Laraba, 15 ga watan Yuli ne dai aka saki Ibrahim Magu, kamar yadda jaridar Premiun Times ta wallafa.

An saki Magu ne da yammacin yau bayan ya shafe kwanaki 10 a tsare.

Wannan shine mako na biyu da fara binciken Magu bisa zarginsa da almundahana da kuma rashin biyayya, kamar yadda ministan shari'a, Abubakar Malami, ya rubuta korafi a kansa zuwa fadar shugaban kasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel