Kwararren makaniki ya yi abin da ba a taba gani ba, ya kera motar da ake tukawa ta bai-bai

Kwararren makaniki ya yi abin da ba a taba gani ba, ya kera motar da ake tukawa ta bai-bai

  • Wani makaniki mai matukar basira, Rick Sullivan ya kirkiro motar da ba a taba ganin irin ta ba.
  • Wannan motar da babu irinta a gari, tana da tayoyi 8, sannan tana tafiya ne ta bai-bai a kan titi.
  • Rick Sullivan ya dauki watanni shida yana kera wannan mota, ya kuma ce ba zai taba saida ta ba.

United States - Wani fasihin mutum mai suna Rick Sullivan ya kirkiro wata mota wanda ba a taba ganin irin ta ba. Wannan ya faru ne a kasar Amurka.

Legit.ng tace Rick Sullivan ya kera wata mota da take tafiya a bai-bai. Wannan mutumi da makaniki ne, yace motar ba za ta taba shiga kasuwa ba.

Kamar yadda muka samu rahoto a ranar Litinin, 8 ga watan Nuwamba, 2021, Mista Rick Sullivan ya shafe tsawon wata da watanni yana aikin wannan mota.

Read also

Budurwa ta shararawa Saurayinta mari gaban Daliban jami'a da ya nemi sanya mata zobe

Ita dai wannan mota tana kama da sauran motocin da aka saba gani, sai dai tana da tayoyi takwas ne – akasin tayoyi hudu da aka sa sauran motoci da su.

Bayan haka kuma wasu bangarorin motar a bai-bai suke, ba kamar yadda aka san sauran motoci ba.

Motar kwararren makaniki
Rick Sullivan dauke da kare a cikin motarsa Hoto: www.dailymail.co.uk
Source: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tayoyi hudu ga hudu

Motar Rick Sullivan tana dauke da tayoyi hudu dabam, bayan hudun da aka san motoci da su. Wadannan tayoyi suna ta bai-bai, kuma suma suna juyawa.

Baya ga tayoyin wannan mota da suka ba mutane mamaki, tana dauke da kofofi a jirkice. Sannan farantin lambar motar da Sullivian ya kera ma a bai-bai yake.

Ba za ni saida mota ta ba

Da aka tambayi Sullivan, wannan kwararren makanikin yace ya dauki watanni shida yana wannan aiki, kuma sam bai da niyyar kai motar ta sa kasuwa.

Read also

Sabon hoton Mufti Menk sanye da babbar riga ya janyo cece-kuce

Wani bidiyo da Ridiculous Rides ya wallafa a Facebook, ya nuna wannan mutumi yana tuka motarsa a titi, inda mutanen gari suka fito kallon abin mamaki.

Rahoton yace mutane sun fito suna daukar hoton abin da ba su taba gani ba. Wata mata da ta ga wannan mota, tayi sha’awar cewa za ta so ta mallaki irinta.

Mai neman aure ya samu mari

Kuna da masaniya cewa wata budurwa ta shararawa saurayinta mari gaban Daliban jami'ar Ambrose Ali da ya nemi sanya mata zobe, da nufin su auri juna.

A maimakon wannan budurwa ta karbi zoben saurayin na ta, sai kurum aka ga ta sharara masa mari. Wannan abu ya ba kowa mamaki, har aka dauke su bidiyo.

Source: Legit.ng

Online view pixel