Budurwa ta shararawa Saurayinta mari gaban Daliban jami'a da ya nemi sanya mata zobe

Budurwa ta shararawa Saurayinta mari gaban Daliban jami'a da ya nemi sanya mata zobe

  • An ga abin ban mamaki yayin da wata daliba ta ki karbar tayin da saurayinta yayi mata na aure.
  • A maimakon wannan budurwa ta karbi zoben saurayin na ta, sai kurum aka ga ta sharara masa mari.
  • Wannan lamarin ya faru ne a jami’ar nan ta Ambrose Alli University (AAU), da ke garin Ekpoma.

Edo - Wani abin al’ajabi ya auku a wata makaranta, inda wani matashi ya buge da shan mari a lokacin da yake sa ran buduwarsa ta yarda za ta aure shi.

Yayin da wasu matan suke rungumar masoyansu a lokacin da suka bijiro masu da zancen aurensu, wannan Bawan Allah dai ya sha mari gaban mutane.

A wani bidiyo da Siggy News ya wallafa a YouTube, an ga wannan saurayi ya cigaba da tsugunawa cak bayan sahibar ta ki amincewa da batun aurensa.

Kara karanta wannan

Wani ɗan sanda ya kashe abokan aikinsa ƴan sanda 4, ya kuma yi wa wasu 3 mummunan rauni

Wannan faifen bidiyo ya nuna budurwar ta ji haushin kawo mata maganar auren da saurayinta ya yi, duk da mutane suna ta zuga ta cewa ta ce ta yarda da shi.

Kafin a ce komai, sai wannan mutumi ya ji mari mai zafi a kumatunsa, wanda ya ba kowa mamaki.

Shi kan shi saurayin ya ji mamakin wannan abin kunya da ya jawowa kansa, ya tsaya nan wurin a tsugune cak, ya gagara motsawa, yana tunanin abin da ya faru.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton yace ana zargin wannan lamari ya faru ne a jami’ar Ambrose Alli da ke garin Ekpoma, jihar Edo.

Budurwa ta shararawa Saurayinta mari gaban Daliban jami'a da ya nemi sanya mata zobe
Budurwa da Saurayinta Hoto: Siggy News
Asali: UGC

Me mutane suka ce da suka ga bidiyon?

Mutane sun yi ta tofa albarkacin bakinsu game da wannan abin da ya faru. Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin abin da mutane suke cewa a shafin sada zumunta.

Kara karanta wannan

'Dan sanda ya daɓa wa abokin aikinsa wuƙa ya yi sanadin ajalinsa

LeeSantos yace:

“Duk wahalar da aka sha a makaranta. Neman aure ne ya zo masa a rai. Kamata ya yi a ce yarinyar ta hada masa da rankwashi a tsakiyar kai.”

GboyegaD cewa ya yi:

“Idan ba ta murna da neman auren ta da ka yi, ka mike tsaye, kayi gaba, ka huta da takaici. Ban san meya kai dayan gwiwarsa kasa ba, ya zama maroki.”

Kasashen Duniya za ta ba Zamfarawa agaji

Tsohon firayim Ministan kasar Birtaniya, Tony Blair ya sha alwashin jawo kasashen Duniya su kawowa jihar Zamafara agaji daga matsalar rashin tsaro.

Gwamna Bello Matawalle ta bakin babban hadiminsa, Zailani Bappa ya bayyana wannan bayan ya hadu da Tony Blair a cibiyarsa da take birnin Landan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel