Dakarun sojojin Nigeria na can suna musayar wuta da 'yan Boko Haram a Borno

Dakarun sojojin Nigeria na can suna musayar wuta da 'yan Boko Haram a Borno

  • Sojojin Nigeria suna can suna musayar wuta da yan ta'addan kungiyar Boko Haram a kauyen Tamsukawu a jihar Borno
  • Wata majiya daga sojoji ta ce yan ta'addan sun kutsa kauyen ne da nufin kai hari sansanin sojoji amma sojojin suka taka musu birki
  • Rahotanni na cewa an tura sojojin sama da wasu sojojin na kasa domin su taimakawa sojojin da ke fafatawa da yan ta'addan a Tamsukawu

Jihhar Borno - Dakarun sojojin Nigeria suna can suna musayar wuta da yan ta'addan kungiyar Boko Haram a kauyen Tamsukawu da ke karamar hukumar Kaga na jihar Borno.

Wata majiya daga sojoji ta shaidawa jaridar The Cable cewa a yanzu sojojin suna fafatawa da yan bindigan.

Dakarun sojojin Nigeria na can suna musayar wuta da 'yan Boko Haram a Borno
Sojojin Nigeria na can suna musayar wuta da 'yan Boko Haram a Borno. Hoto: The Cable
Source: Facebook

Read also

Yan ta'addan Boko Haram 17,000 suka mika wuya kawo yanzu, Kwamdanda Operation Hadin Kai

Ya ce yan ta'addan sun kutsa garin domin kai wa sojojin hari da yamma, amma ba su yi nasara ba domin sojojin sun dakile harin kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kawo yanzu ba a tabbatar da adadin wadanda suka mutu ba.

Rahotanni sun ce an tura sojojin sama da wasu dakarun sojojin daga Ngamdu domin su kaiwa sojojin dauki.

Sojoji na cin galaba kan yan ta'adda, Lai Mohammed

A baya-bayan nan gwamnatin tarayya tace tana cin galaba kan yakin da ta ke yi da yan ta'addan a arewa maso gabas.

Lai Mohammed, ministan labarai da al'adu, cikin wata hira da aka yi da shi a ya ce mika wuya da sojojin ke yi na nuna cewa ana samun zaman lafiya a yankin na kudu maso gabas.

Ya kara da cewa sojojin sun tsananta 'hare-haren' da suke kai wa yan ta'addan hakan ke basu daman cigaba da mamaye yankunan da yan ta'addan suka da gindin zama.

Read also

Babbar Magana: Sojoji sun janye sun bar yan sanda da aikin tsaro baki daya a wannan jihar

Sokoto: 'Yan ta'adda sun naɗa sabbin hakimai da dagatai, sun bude kasuwanni da gwamnati ta rufe

A wani labarin, yan ta'adda da aka fi sani da yan bindiga sun nada wasu mambobinsu a matsayin dagatai a wasu kauyuka a karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

A cewar wata jaridar intanet ta Sokoto, Daily Star, kasurgumin shugaban yan bindiga, Turji ne ya nada sabbin dagatan.

Rahoton ya ce an fara kiran yan ta'addan su kira yan kauyen Gangara su hallarci taro a kauyen Suturu a ranar Alhamis inda aka sanar da sauke tsaffin dagatan sannan suka nada mambobinsu a matsayin sabbin shugabanni.

Source: Legit.ng

Online view pixel