Tsohon Gwamna ya bada labarin yadda ya sasanta Janar Babangida da Buhari a shekarar 2005

Tsohon Gwamna ya bada labarin yadda ya sasanta Janar Babangida da Buhari a shekarar 2005

  • Orji Uzor Kalu ya bada labarin kokarin da ya yi na sasanta Muhammadu Buhari da Ibrahim Babangida.
  • Tsohon gwamnan na Abia yace kafin ya yi masu sulhu a 2005, tsofaffin sojojin ba su magana da junansu.
  • Marigayi Odimegwu Ojukwu da Marigayi Dr. Alex Ekwueme sun halarci wannan taro a garin Igbere.

Nigeria - Shugaban masu tsawatarwa a majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu, yace ya taba hada taro domin ya sasanta Muhammadu Buhari da Ibrahim Babangida.

A ranar Juma’a, 5 ga watan Satumba, 2021, Sanata Orji Uzor Kalu yace a shekarar 2005 ya hada tsofaffin shugabannin domin ya sulhunta su a lokacin ba a shiri.

Orji Uzor Kalu ya bayyana wannan ne da ya daura hoton dattawan kasar a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Na daina zuwa Coci saboda Faston kullum zagin Buhari yake yi, Femi Adesina

Uzor Kalu ya fito da wannan hoto ne a Facebook a ranar Alhamis domin ya tuna da Marigayi Odimegwu Ojukwu wanda ya mutu a shekarar Nuwamban 2012.

Tsohon gwamnan na jihar Abia ya kuma bayyana cewa ya yi amfani da wannan dama wajen zama da Marigayi Dim Odimegwu Ojukwu da Dr. Alex Ekwueme.

Da yake maidawa mutane martani a shafin na sa, Sanatan na Abia ta Arewa, yace hoton da ya sa yana dauke da Buhari, Babangida, Ekwueme, Ojukwu da Kalu.

Janar Babangida da Buhari a shekarar 2005
Buhari da wanda ya kifar da gwamnatinsa, Babangida a 1985 Hoto: thenewsguru.com
Asali: UGC

Sanatan ya tabbatar da cewa hoton ba na bogi bane kamar yadda wasu suke neman su nuna a dandalin.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Ekwueme da mutumin da ya jagoranci yakin Biyafara, Ojukwu sun halarci wannan zama da aka yi domin ayi sulhun.

Kara karanta wannan

Gwamnan Legas ya je wurin da bene ya ruguje domin ganewa idonsa abin da ya faru

Jawabin da Orji Uzor Kalu ya yi a Facebook

“Ina kwana abokai na. Na karanta martanoninku da ke nuna cewa wannan hoto da na wallafa na karya ne. A’a, ba haka ba ne.” - Orji Uzor Kalu.
“An dauki hoton ne a 2005 a kauyenmu, Igbere a lokacin da na samu damar sasanta shugabanni na, Marigayi Dim Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu, da shugaban kasa Muhammadu Buhari, tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Babangida, da mataimakin shugaban kasa, Alex Ekwume da ya rasu."
“Kafin ayi wannan sulhu shugaban kasa Muhammadu Buhari, da Janar Ibrahim Babangida ba su magana da juna.”

Osinbajo ya jagoranci taron FEC

A makon nan aka ji cewa gwamnatin Najeriya za ta kashe Biliyoyin kudi domin inganta tsaro a filin jirgin sama na MMIA da ke Legas da gyaran wani titi a Sokoto.

A zaman FEC na makon nan, an amince za a kashe kudi wajen wasu ayyukan gyaran titi da gina katafaren dakin taro a Jami’ar Abuja da sayen kayan aiki a FMC Jabi.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Hawaye sun kwaranya yayin da Najeriya ta sake rashi na wani tsohon sanata

Asali: Legit.ng

Online view pixel