Gwamnan Legas ya je wurin da bene ya ruguje domin ganewa idonsa abin da ya faru

Gwamnan Legas ya je wurin da bene ya ruguje domin ganewa idonsa abin da ya faru

  • Gwamnan jihar Legas, Sanwo-Olu ya ziyarci wurin da ginin bene mai hawa 22 ya ruguje a jihar Legas
  • Gwamnan ya ziyarci wurin domin ganewa idonsa yadda lamarin ya faru da misalin karfe daya
  • Ginin bene mai hawa 22 ya ruguje a Ikoyi ta jihar Legas, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da yawa

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya isa wurin da ginin bene mai hawa 22 a Ikoyi ya ruguje.

Rahotanni sun nuna cewa Sanwo-Olu ya ziyarci wurin da lamarin ya faru a yau da misalin karfe 1 na rana.

Kafin isowar gwamnan, an fitar da wasu gawarwaki biyu daga baraguzan ginin da ya ruguje, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa 22, PM News ta ruwaito.

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Legas ya je wurin da bene ya ruguje domin ganewa idonsa
Ginin da ya ruguje a jigar Legas | Hoto: thecable.ng
Asali: Facebook

A ranar Talata ne Sanwo-Olu ya bayar da umarnin dakatar da babban manajan hukumar kula da gine-gine ta jihar Legas (LASBCA), Gbolahan Oki.

Kara karanta wannan

Habasha: 'Yan tawaye sun kewaye Addis Ababa, firaminista ya ce kowa ya dauki makami

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bincike ya nuna ana kan ginin ne a lokacin da ya ruguje.

Masu aikin ceto sun ce a ranar Laraba sun gano gawarwaki 22 ya zuwa yanzu tare da ceto mutane tara da suka tsira, amma ma’aikatan ginin na fargabar da dama daga cikin abokan aikinsu sun makale a ciki.

Yadda manyan gine-gine 8 suka ruguje a Najeriya cikin shekaru 15

A wani lamarin, Za a iya tunawa da rugujewar wani babban bene a ranar Litinin, 1 ga Nuwamba, 2021, a matsayin wata rana mai muni ga 'yan Najeriya.

Ginin da ya ruguje a titin Gerald da ke unguwar Ikoyi, wuri ne da ake gina gidaje na alfarma.

Sai dai abin takaici, ba wannan ne karon farko da ‘yan Najeriya ke fuskantar irin wanna, ba, suna mamakin ko me aka yi don hana rugujewar.

Kara karanta wannan

Yan bindigan da suka saci Malamai a Jami'ar Abuja (UniABuja) sun bukaci N300m kudin fansa

Asali: Legit.ng

Online view pixel