Gwamnatin tarayya ta kashe N58.61billion wajen buga takardun kudin Najeriya guda 2.581 bilyan

Gwamnatin tarayya ta kashe N58.61billion wajen buga takardun kudin Najeriya guda 2.581 bilyan

  • Babban bankin Najeriya CBN ke da hakkin fitar da kudin da ake amfani da shi a Najeriya, bisa dokar kasa na sashe 2(b) na CBN Act 2007
  • CBN ya bada umurnin buga sabbin kudade guda bilyan 2,51 na mabanbantan Naira a 2020 domin amfanin jama'a
  • Gwamnatin tarayya ta kashe sama da bilyan biyu da rabi wajen buga wadannan kudade

Abuja - Babban bankin Najeriya CBN ya bayyana yadda aka kashe N58.618 billion wajen buga kudade guda 2.518 billion a shekarar 2020.

CBN ya bayyana hakan a rahoton da ya saki a shafinsa na yanar gizo.

A cewar rahoton. adadin da aka kashe a 2020, ya yi kasa da wanda aka kashe a shekarun 2019 da 2018.

Read also

Gwamnatin tarayya ta kashe N538m wajen zubar da tsofaffin kudi guda1.51bn

A 2018, an kashe N64bn yayinda aka kashe N75bn a 2019.

Rahoton yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Kudin da aka kashe wajen buga kudade a 2020 shine N58.6 billion inda aka hada sa N75.5 billion da aka kashe a 2019. Wannan na nuni ga cewa an samu saukin N16.9 billion."

Gwamnatin tarayya ta kashe N58.61billion
Gwamnatin tarayya ta kashe N58.61billion wajen buga takardun kudin Najeriya guda 2.581 bilyan Hoto: Naira

A ina aka buga wadannan kudade?

CBN ya kara da bayanin cewa an buga wadannan kudade ne a masana'antar buga kudin Najeriya watau (NSPM Plc).

"Masana'antar NSPM Plc aka baiwa kwangilan buga dukkan kudaden. A karshen 2020, (NSPM Plc), ya buga dukkan kudaden da aka amince."

Gwamnatin tarayya ta kashe N538m wajen zubar da tsofaffin kudi guda1.51bn

Babban bankin Najeriya CBN ya ce an yi watsi da takardun kudi bilyan 1.51 na kimanin N698,480 million a 2020.

Wannan na kunshe cikin rahoton shekarar 2020 da sashen ayyukan kudi ta tattara.

A Najeriya, bankin CBN na lalata takardun Nairan da sukayi datti kuma suka yage domin tabbatar da cewa sabbin suka fi yawa hannun mutane.

Source: Legit.ng

Online view pixel